Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
(Shiri na Musamman) Yara da kwallon kafa: "Filin wasa na Yuan 100" na kasar Sin da Kwalejin koyar da taurarin kwallon kafa ta Nijeriya
2019-12-28 14:46:59        cri

Saminu: Masu sauraro, barkanku da sake kasancewa tare da mu a shiri mu na yau, na wasan motsa jiki, Saminu Alhassan ne ke muku barka da war haka. Da fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda lafiya a nan birnin Beijing. Tare da ni a yau cikin shirin na ku akwai Zainab Zhang, da kuma Amina Xu.

Kafin gabatar da su, domin kawo muku tsarabar da suke tafe da ita, sanin kowa ne cewa yara da matasa a yankunan Najeriya na nuna matukar sha'awar kwallon kafa. A ko ina ka shiga kana iya ganin yara na buga kwallo cikin abokai, ko da kuwa ba bu wani mai horaswa na musamman. Kamar ni kai na, yara da matasa da yawa mun taka leda a 'yan kananan filayen wasan kwallo, ko kangwaye ko ma a wasu lokuta kan tituna, duk kuwa da cewa ba mu da wani kwararren kociya, wata kila idan da muna da mai horaswa a wancan lokaci, wasu daga cikin mu na iya zama taurarin kwallon kafa, ko ya kiga gani Amina?

Amina Xu: Hakika hakan abun yake, masu sauraron mu barkan ku da kasancewa tare da mu ta cikin wannan shiri, kamar yadda kuka ji tun da fari, ni ce Amina Xu.

Saminu: barka dai Amina. To da yake kowa ya sani cewa Nijeriya da Sin manyan kasashe ne a bangare kwallon kafa, na san irin yanda jama'a da dama ke bibiyar kulaflikan kwallon kafa na kasa da kasa a nan ma kasar Sin, to amma shin matasan Sinawa na sha'awar buga kwallon kafa kuwa?

Zainab gare ki

Zainab Zhang: Haka ne, assalam alaikum, ni ce Zainab Zhang. Kamar yadda ka bayyana a Najeriya yara da matasa da dama na da matukar kwaunar kwallon kafa, kuma haka abun yake ma a nan kasar Sin.

Saminu: Abokan aikina Amina Xu da Zainab Zhang ke nan. Kuma kamar yadda na fada tun da fari, suna dauke da tsarabar musamman ta cikin shirin na yau,da yake Amina ki taba aiki a tarayyar Nijeriya, kuma labarin da kike dauke da shi na Nijeriyar ne mu fara da shi ko?

Amina Xu: Haka ne, Wannan labara ya kunshi wani mutum ne mai suna Kunle Ismail Apampam, wanda ya kwashe shekaru kusan 20 yana aikin kociyan kwallon kafa a kwalejin Lugbe Football Academy. A cikin dalibansa akwai wasu sabbin taurarin 'yan wasan kwallon kafa a Nijeriya kamar su Mustapha Mohammed, da Dele Ogundare da kuma Abu Aliyu da dai sauransu. Kunle ya kan yi yawo ne kan tituna, don lalubo yara dake da kwarewa wajen wasan kwallon kafa.

"Da farko, muna mai da muhimmanci sosai kan kwarewar yara, ba wanda zai iya kashe hazaka, dole ne mu kara musu kwarin gwiwa, don su nuna hazaka wajen wasan kwallon kafa."

Saminu: To, lallai kuwa Kunle ya yi kama da wani mai zakulo taurarin 'yan wasa, inda dalibansa ke kaiwa matsayi na kwarewa a kwallon kafa. Ke kuma Zainab fa, wane labari kika zo mana da shi?

Zainab Zhang: Mutumin da zan bayyana muku labarinsa shi ne mai horaswa na wasan kwallon kafa na Sin Chen Longqiang. Wannan mutum ya kafa wani filin wasa ne dake kan rairayin bakin teku na musamman, sunansa shi ne "Filin wasa na Yuan 100", wanda yake da burin horar da kananan yara masu sha'awar wasan kwallon kafa a garin. Wadannan yara suna buga wasan kwallon kafa tare da shi a kan wannan filin wasa na musamman, da jin dadin wasan sosai tare da samun kyakkyawan maki a wannan fanni. Har ma wasu yara sun fita daga kauyen don canja rayuwarsu ta wasan kwallon kafa.

Saminu: Kai, wadannan labarai suna da ban sha'awa sosai, kowa zai so sanin me ya faru a kwalejin Lugbe, da kuma "Filin wasa na Yuan 100" .

Amina gare ki

Amina Xu: Kwalejin Lugbe na karkarar Abuja, gwamnati ta samar musu wani fili kyauta, don su rika samun horo. Amma, ba su da na'urori masu inganci na samun horo. Fili ne wanda hasken rana ke sauka kai tsaye a kan sa, wasu wuraren na da dan lebir, don haka mika kallo tsakanin 'yan wasa na tattare da kalubale. An yiwa filin layuka da farin launi, ba komai a jikin karafan raga sai yagaggiyar raga dake lilo a jiki, da wani dan wuri mai 'yar runfa inda yaran ke iya hutawa. Kasar wurin cike take da duwatsu da tubalin jar kasa.

Saminu: Lallai, yanayi ne mai wuyar gaske, ana iya horar da taurarin 'yan wasa a cikin irin wannan yanayi, abun da wahalar gaske. Ya kika ce Zainab.

Zainab Zhang: Hakika yanayin yankin Lugbe ba shi da kyau, amma labarin da na fara kawo muku ya faru ne a garin Xiapu dake lardin Fujian na kasar Sin, shi ma yanayin wurin da matasan ke samun horo ba shi da kyau. Da farko dai babu sandunan raga na wasan kwallon kafa a rairayin bakin teku, saidai Chen Longqiang ya yi amfani da kayan soso da duwatsu a matsayin turakan gola biyu na wasan. Sai dai kuma abu ne mai wuya a bambanta ko kwallo ta shiga raga ko a'a. Bayan gama horaswarsu a wata rana, a kan hanyar koma gidansa, Chen Longqiang ya gano wani kantin sayar da bututun roba, lamarin ya maida Chen Longqiang ya yi tunani cewa, ana iya kafa turakan gola guda biyu ta hanyar amfani da bututun roba.

"Na auna fadi da tsayin turakan gola na wasan kwallon kafa, sa'an nan na sayi bututun roba guda shida don kafa turakan gola biyu. Yana da sauki kafa su a yayin da za a fara buga wasan, da kuma ajiye su bayan da aka gama horaswa. Tun da muka samu irin wadannan turakan gola biyu, filin wasanmu ya yi kamar hakikanin filin wasan kwallon kafa. Yawan kudin da aka kashe wajen sayen su bai wuce Yuan 100 kacal ba."

Don hakan, filin wasa na Yuan 100 ya fito.

Saminu: To lallai wannan suna wato"Filin wasa na Yuan 100" na kunshe da dabara wajen kirkirar sa, da kuma kaifin basira sosai. Idan na fahimci batun da kyau, kwalejin Lugbe na kokarin bullo da taurarin 'yan wasan kwallon kafa ne, to Zainab akwai wani karin bayani game da wannan fili na "Filin wasa na Yuan 100"?

Zainab Zhang: Kwarai kuwa, tun bayan kafa filin wasa na Yuan 100, karin kananan yara suna zuwa don buga wasan kwallon kafa tare da Chen Longqiang. Don haka, Chen Longqiang ya kafa wata kungiyar wasan kwallon kafa mai suna "Changfeng", wato iska a kan teku da Hausa. Wannan suna ya zo daga wakar mashahurin mai rubuta wakoki na daular Tang na kasar Sin Li Bai, ma'anarsa ita ce koda yake ana fuskantar kalubale, amma an yi imani da cewa za a cimma buri a nan gaba ta hanyar yin kokari. Ma'anar ta dace da yanayin kungiyar Chen Longqiang. Akwai yara fiye da 10 a cikin kungiyar "Changfeng", shekarunsu suna daban daban. Ban da yanayin mahaukaciyar guguwa, su kan buga wasan kwallon kafa a kan filin wasan har na tsawon awoyi biyu ko uku. A lokacin da aka gama horaswa a kowace rana, Chen Longqiang na kai dukkan yaran zuwa gidajensu bi da bi. Kafin ya kammala kai su gida kuwa, lokaci zai zarce karfe 10 na dare. Ga wadannan yara, Chen Longqiang ba ma malaminsu ne kawai ba, wani abokin su ne, yaran da yake koyarwa su kan kira shi da sunan "dan uwa Long".

Saminu: Lalle wadannan yara sun ci gajiyar horo na kwarewa a kwallon kafa sosai. Amma kin ce Chen Longqiang mai fasahar sassakar dutse ne, ba kamar Kunle wanda ya dade yana aikin kociya har tsawon shekaru 20 ba, tun da Chen ba shi da kwarewa sosai wajen horar da yara, ko me yasa ya zama kociya? Ba ya tsoron mutane su ce yana yaudara kasancewar sa ba shi da horo na kwarewa?

Zainab Zhang: Eh, haka ne, amma ka san cewa fa, mutane a kewayen Chen Longqiang ba su fahimci dalilin da ya sa baligi kamar Chen Liongqiang zai rika buga wasan kwallon kafa tare da kananan yara ba. A ganinsu, Chen Longqiang ba shi da aikin yi. Har ma iyalansa ba su amince da hakan ba a farko. Amma Chen Longqiang ya kiyaye yin horaswa tare da yara, kana yaran da yake koyarwa suna son wasan kwallon kafa sosai, kana a gasanni suna samun maki mai kyau, daga baya kuma mutane sun fara nuna amincewa gare su. Haka kuma iyalan Chen Longqiang sun fara canja ra'ayinsu, suna ganin cewa, hanyar da Chen Longqiang yake bi hanya mai dacewa. 'Yar innar Chen Longqiang mai suna Li Fang ta bayyana cewa:

"Da farko, mun ki amince da shi, domin yana buga wasan kwallon kafa amma bai gudanar da aikin kansa ba. Amma a halin yanzu, mun canja ra'ayinmu, mun gane a hakika dai wasan kwallon kafa yana samar da taimako ga kananan yara."

Yaran da Chen Longqiang yake koyarwa suna son buga wasan kwallon kafa a kan rairayin bakin teku sosai, wasan yana kawo jin dadi gare su, kana ya samar da hanyar yin rayuwa ta daban gare su. A cikin wasu shekarun da suka gabata, yaran kungiyar Changfeng da dama sun zama muhimman membobin kungiyar wasan kwallon kafa ta makarantunsu, har ma wasu daga cikinsu sun shiga kungiyar wasan ta garin Xiapu.

An haifi Chen Xiaohong a shekarar 2015, wanda ya fara yin horaswa tare da Chen Longqiang a aji na hudu na makarantar firamare. A sakamakon kwarewarsa da kokarinsa, an shigar da Chen Xiaohong a cikin kungiyar wasan kwallon kafa ta garin Xiapu, a yayin aji na shida na makarantar firamare nasa. Kana domin wasan kwallon kafa, an shigar da shi zuwa makarantar midil mai kyau ta garin. Chen Xiaohong ya ce, ba ma fasahohin wasan kwallon kafa da malam Long ya koya masa kawai ba, hatta ma ya koya masa yadda za a cimma burinsa ta hanyar yin kokari. Chen Xiaohong ya ce,

"Na koyi fasahohin buga wasan kwallon kafa daga wajen malam Long, ina da burin zama dan wasan kwallon kafa, malam Long shi ma nuna mini yadda zan cimma buri na. A halin yanzu, zan koma buga wasan kwallon kafa tare da shi idan ina da lokaci."

Saminu: To, lallai Chen Longqiang mutum ne mai mutunci. Yara da ya horar ba ma kawai sun sami kwarewa sosai kan wasan kwallon kafa ba ne, har ma suna hazaka a makaranta, Kwallon kafa tamkar wani wasa ne dake kara musu karsashi a rayuwarsu, haka su ma yaran kwalejin Lugbe na da buri zama tauraron wasan kwallo kafa, suna kokarin horar da kansu, ko ba haka ba Amina?

Amina Xu: Kunle ya fahimci wannan batu. A ganinsa, wasan kwallon kafa ba wani aiki ne na tsawon rayuwa ba, wadanda suke da sa'a za su zama 'yan wasan kwallon kafa masu shahara. Wani muhimmin aiki na Kunle shi ne baiwa dalibansa karin zabi, wato idan wasu ba su iya zama 'yan wasa ba, ko idan sun zama 'yan wasa amma sun tsufa ko sun ji rauni, za su iya kama wani aiki na daban. Saboda haka, Kunle na mai da hankali sosai kan karatun yara: Ya ce: 

"Na gano yawancin yara daga tituna, na yi alkawari ga iyalansu cewa, yaran za su je makaranta. Saboda samun ilmi na da muhimman kwarai. Wannan aiki ne da na kwashe shekaru 20 ina gudanar da shi, zan kuma ci gaba. Dalibaina suna wasa a kulob daban-daban a kasar nan."

Kwalejin na da yara maza kimani 50, sun kuma kasu gida uku, akwai rukunin 'yan shekaru 8 zuwa 10, da na 11 zuwa 15, da kuma na 15 zuwa 22. Ana fara horo tun sassafe, ta yanda za su iya komawa gida, su yi wanka sun ci abinci kuma su tafi makaranta. Kaza lika kwalejin, ba ta horar da yara cikin dare, saboda tabbatar da cewa, yaran sun samu lokacin dukufa kan koyon ilmi. Ko wace Juma'a da Asaba da Lahadi, yara masu hazaka za su fito su sami damar cimma burinsu.

Kunle ya bayyana cewa, wasu yara suna cikin mawuyancin hali, iyalansu ba su da kudin saya musu kwallon kafa, sai dai su yi amfani da wata kwalaba ko duk wani abu da suka samu ya zama abun samun horo. Amma, kwallon kafa na basu babban sauyi da ma iyalansu. 

"Yara a kwalejinmu, iyalansu na cin gajiyar kwallon kafa, wanda ya canja rayuwarsu, saboda yara suna iya dogaro da kansu bisa kwallon kafa, da samar da kudi da abinci."

Kunle ya ce, ya gano Mustapha Mohammed a kan titi, yana wasa, ba shi da komai a waccan lokaci sai talauci. Bayan ya shiga kwalejin, ya yi kokari sossai, har ya shiga kungiyar Pillars ta Kano, daga baya kuma ya koma Gombe United, daga bisane ya shiga Sunshine Star ta Akure. Kudin shiga na Mustapha Mohammed ya kai Naira dubu 300 ko fiye. Idan wani kulob ya zabi yara daga kwalejin, shi ma Kunle zai samu 'yan kudi.

Saminu: Ga alama kwalejin Lugbe na bin salo irin na kasuwa ne, amma ba su mai da zama dan wasa kwararre hanya daya tak da za su bi, kasancewar suna da burin yaran da suka horas su iya dogaro da kan su, ko da ba ta hanyar kwallo ba, abun na da ban sha'awa. To amma shin kwalejin na horar da taurarin 'yan wasa da dama kuwa?

Amina Xu: Kwarai kuwa, na gano wani yaro mai suna Alamesia, ba da dadewa ba ya kammala horarsa, yana rike da kwallon kafar da karfin gaske, ya kuma gaya mini cewa: 

"Kwallon kafa ta sauya min rayuwa. Ta raba ni da titi. a baya ba ni da abun yi, koci ya ganni, ya saka ni a cibiyar samun horo, ya koya min abubuwa da yawa. Ina son zuwa kulob da dama, kuma ina son buga kwallo a Manchester united kamar ASHLEY Young. "

Saminu: Tabbas yaro ne mai matukar son ci gaba, ina ma alamecia ya gano burin sa tun da wuri?. A yau labaran nan biyu na Amina da Zainab sun taba zuciya ta matuka. Son kwallon kafa ya yi tasiri matuka a kasashen nan biyu masu nisa da juna.

Ko a dan karamin wurin wasa, ko a katafaren filin kwallo na zamani, yara na iya cimma burin su na zama taurari ta hanyar buga kwallon kafa. Ba wanda ya san adadin yawan makarantun dake Najeriya, kamar dai kananan cibiyoyin koyon kwallon kafa. A duk shekara, yara masu hazaka ba iyaka, suna shiga matakin farko na kwalejin koyon kwallon kafa, a wasa wanda wasu ke samun sa'ar yin fice a cikin sa, har su kai ga zama taurarin kwallon kafa ", akwai 'yan wasa masu hazaka a Najeriya, saboda "fiffiken mikiyar Afirka" wato lakabin babbar kungiyar kwallon kasar, na taka rawar gani a wasannin kasa da kasa. Kaza lika a daya hannun, akwai daruruwan yara dake buga wasa a cibiyar "yuan dari" wadda ke can daura da gabar ruwan gabashin Sin. Long ge da sauran samarin sa, na ci gaba da samun horo a kullum. Long ge ya san cewa, wata rana yaran za su bar wannan kauye, domin shiga sauran sassan duniya. Yana fatan za su tuna da shi, su dawo domin buga kwallo tare da shi.

To, masu sauraro, da wannan mu kawo karshen shiri namu na yau na wasan motsa jiki, sai mako mai zuwa.

Amina Xu/Zainab: Kun huta lafiya, sai mako mai zuwa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China