Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Sin na aiki tukuru wajen yayata manufar ci gaban duniya na bai daya
2019-12-31 21:27:25        cri

A yau jajibirin sabuwar shekara, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabin murnar shiga sabuwar shekara ta 2020, jawabin da aka yada ta babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da kuma internet. Cikin jawabin nasa, shugaba Xi ya yi bitar nasarorin da Sin ta samu cikin shekarar 2019, tare da fatan samun karin ci gaba a shekarar 2020.

Ga kasar Sin da ma sauran sassan duniya, shekarar 2019 ta bambanta da sauran shekaru. A wannan shekara, yayin da manufofin daukar matsayar kashin kai, da kariyar cinikayya, da ma karin takun saka a fannin takarar cinikayya suka karu, dukkanin kasashe na fuskantar matsi gwargwadon karfin su ta fuskar neman ci gaba. A wannan shekara ne kuma Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ta cika shekaru 70 da kafuwa. Yanzu haka dai duniya ta zuba ido domin ganin shin ko kasar Sin dake matsayi na biyu a fannin karfin tattalin arziki, za ta iya jure matsi daga sassan wajenta ko a'a, da ma ko za ta iya cimma muradun ta na ci gaba a kan lokaci, kana ko za ta iya dorawa wajen jagorantar tattalin arzikin duniya ko akasin haka. Game da wadannan tambayoyi, shugaba Xi Jinping ya amsa da cewa, a shekarar 2019, an yi hasashen ma'unin GDPn kasar Sin zai kai kusan yuan triliyan 100, kana matsakaicin kudin shigar daidaikun al'ummar kasar zai kai dalar Amurka dubu 10. Wadannan alkaluma guda biyu an yi aiki tukuru kafin cimma nasarar su, kana suna da matukar alfanu. Ya ce hakan ya nuna irin ci gaba da Sin ke samu, inda ta daga daga matsayin kasa mai matsakaicin kudin shiga, zuwa kasa mai yawan kudin shiga, wanda hakan zai bunkasa karfin 'yan kasar na sayayya, da gudanar da bukatun yau da kullum, kaza lika hakan zai fadada kasuwar kasar ga sauran sassan duniya.

Irin ci gaban da aka samu nasarar sa a shekarar 2019, ya nunawa duniya irin salo da karfin ikon Sin. Akwai wasu dalilai na zahiri masu nasaba da wannan ci gaba, wato batun gudanar da gyare gyare a cikin gida, da bude kofa ga waje, da kirkire kirkire. Shugaba Xi Jinping ya yi bitar manyan nasarorin da Sin ta cimma cikin sakon sa na taya murnar sabuwar shekara, Ciki hadda kammala aiwatar da sauye sauye ga JKS da bangaren gwamnati, da rage haraji da kudaden da ake kashewa wajen ayyukan gudanar da sana'o'i da kusan sama da yuan triliyan 2, da kara yawan yankunan cinikayya cikin 'yanci na gwaji, da bunkasa kirkirar fasahar sadarwa ta 5G, da harba tauraron dan Adama na Chang'e-4, da cimma nasarar sauka a bangaren wata mai nisa, wanda ya kasance karon farko a tarihin bil Adama. Kaza lika an yayata dabarun samar da ci gaba mai inganci, wanda hakan ya nunawa duniya cewa, manufar kasar Sin ta gudanar da sauye sauye a gida, da bude kofa ga kasashen waje, ba wai magana ce kawai ta fatar baki ba.

A shekarar 2020, Sin za ta ci gaba da aiki tukuru, da salon kaiwa ga nasara ta hanyar zaman lafiya, da yin komai a bude, za ta kuma kara azama wajen kaiwa ga nasarar kudurorin ta, da aiki tare da sassa masu ruwa da tsaki, wajen gina manufofin dake karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya" tare da sauran kasashe, kana za ta yayata manufar gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil Adama. Wannan ba wai buri ne na ci gaban kasar Sin ita kadai ba, domin kuwa wani alkawari ne da Sin din ta dauka ga duniya baki daya a wannan sabuwar shekara dake tafe. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China