Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoton da Jaridar New York Times ta bayar game da yaran Xinjiang cike yake da karya da jita-jita
2019-12-31 10:23:32        cri

Babban gidan rediyo da telibijin kasar Sin CMG ya rubuta wani sharhi mai taken "rahoton da Jaridar New York Times ta rubuta kan yaran jihar Xinjiang cike yake da karairayi da jita-jita", sharhin ya ce, jaridar ta ba da labarin cewa, wai gwamnatin kasar Sin ta tilastawa yaran jihar Xinjiang zuwa makarantar kwana, inda ta tilasta musu rabuwa da iyalansu, da kuma koyon Sinanci a maimakon yarensu, kana da cusa musu ilimin kaunar kasar Sin don cusa musu wata akida . Wannan rahoto yaudara ce da jaridar ta bayar bisa tunaninta, kuma babu gaskiya a ciki.

Bayanin ya nuna cewa, ba da dadewa ba wata kafar yada labaru ta kasar Burtaniya ta wallafa wani labarin karya cewa, wata yarinya dake zaune a birnin London mai shekaru 6 da haifuwa ta gano sakon neman ceto a jikin wani katin Kirsimeti da ta ce wai fursunan ketare da aka tsare a gidan kurkuku na kasar Sin ne suka rubuta. A wannan karo kuma, jaridar New York Times ta rubuta wani labarin karya daban kan yaran jiyar Xinjiang, matakin da ya nuna cewa, fakewa da sunan yara ya zama wani sabon mataki da kafofin yada labarai na kasashen yamma suke amfani da shi wajen shafawa kasar Sin kashin kaza, ta yadda za su jawo hankalin mutane ta hanyar tayar da hankalin mutane.

 

Sharhin ya kara da cewa, shafawa cibiyoyin koyon fasahohin sana'o'i ta jihar Xinjiang bakin fenti, da illata tsarin ba da ilmi a wurin, wani yankuri ne da wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma suke yi don katse dangantakar Xinjiang da sauran yankunan kasar Sin wajen samun bunkasuwa, da kuma rura wuta tsakanin al'umomin kasar Sin, don cimma mummunan burinsu na hana bunkasuwar kasar Sin. Amma, duk da wadannan matakan da suka dauka, gaskiya ba za ta buya ba. Sin za ta yi iyakacin kokarin samun bunkasuwar daukacin al'umominta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China