Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ga yadda Xi Jinping ya gayyaci abokan kasa da kasa da su ziyarci Sin a shekarar 2019
2019-12-27 14:10:58        cri


A karshen wannan shekara ta 2019, za mu gabatar da bitar wasu harkokin diflomasiyya na kasar Sin na bana. Harkokin diflomasiyya da shugabannin kasar Sin suka yi a shekarar 2019 sun hada da babban tarukan diflomasiyya guda 4, da ziyarar aiki a kasashen ketare sau 7, da kuma tarukan ganawa ko tattaunawa tsakanin bangarori daban daban sama da dari daya.

Kasar Sin dake cikin wannan sabon zamani, ba wanda zai iya hana neman ci gaba kan harkokin diflomasiya.

A halin yanzu, ana fuskantar babban sauyin yanayin duniya, wanda ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru sama da dari daya da suka gabata. Shugaba Xi Jinping ya ce, babu wata kasa da ita kanta za ta iya warware dukkanin kalubalolin dake gabanta ba, kuma hanyar bude kofa ga waje, da yin hadin gwiwa ita ce hanya kadai da kasa da kasa za su bi. "Dabarar Sin" mai cike da basira za ta samar wa kasa da kasa sakamako masu gamsuwa, har ma hakan ya kara musu fahimtar kasar Sin.

A ranar 5 ga watan Nuwamba na shekarar 2019, an sami wasu baki na musamman a Lambun gargajiya na Yuyuan dake birnin Shanghai na kasar Sin. Shugaba Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan sun gayyaci shugaban kasar Faransa da uwargidansa zuwa wannan lambun shan iska, tare da kallon wasan kwaikwayo na wakar Kunqu, da wasan kwaikwayo na gargajiya na Yue na lardin Zhejiang na kasar Sin. Xi Jinping ya gaya wa Emmanuel Macron, wanda karo na farko ya kai ziyara birnin Shanghai cewa, yadda birnin Shanghai yake kasancewa ya nuna sakamakon da kasar Sin ta samu ta fuskar bude kofa ga waje da neman ci gaba, ya kuma nuna canjawar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen ketare daga shekarar 1840 har zuwa yanzu. Xi Jinping ya kuma nuna fatan cewa, ziyarar shugaba Macron a kasar Sin ta wannan karo, za ta iya kara fahimtarsa kan birnin Shanghai, har ma da kasar Sin baki daya.

Shugaba Macron ya ce, lalle birnin Shanghai ya burge shi sosai, a wannan birni ya san yadda kasar Sin ke bude kofa ga waje, da kuma kyakkyawar makomar da kasar za ta samu.

Yadda aka shirya ziyarar shugaba Macron a kasar Sin ya nuna tunanin shugaba Xi, kan yadda za a raya dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Faransa. Yayin taron shawarwari dake tsakanin shugabannin biyu da aka yi a rana ta biyu, shugaba Xi ya bayyana cewa, "A halin yanzu da ake fuskantar babban sauyin yanayin duniya, wanda ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru sama da dari daya da suka gabata. A matsayin zaunannan mambobi a kwamitin sulhu na MDD, da wakilan al'adu na gabashi da yammacin kasashen duniya, ya kamata kasar Sin da kasar Faransa, su dauki karin nauyi da kuma nuna wa kasa da kasa babban nauyin da ya kamata kowace babbar kasa ta dauka. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Faransa kan harkokin kasa da kasa, da harkokin makomar su, da ma harkokin al'umma, domin kyautata dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Faransa zuwa wani sabon matsayi, ta yadda kasashen biyu za su ci gaba da kasance gaba cikin manyan kasashen duniya."

Shekarar 2019 shekara ce da kasa da kasa ke mai da hankali kan dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Faransa. Sabo da wannan shekara ita ce shekarar cika shekaru 55 da kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu. A wannan shekara ta musamman, shugabannin kasashen biyu sun kai ziyara ga juna, inda suka jaddada babban nauyin dake gabansu a matsayin manyan kasashen duniya, da kuma dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu. Sun ce, ya kamata kasashen biyu su ba da karin gudummawa ga kiyaye zaman lafiya, da zaman karko na kasa da kasa.

Haka kuma, cikin mu'amalar da shugabannin biyu suka yi, akwai wasu lokutan da suka burge jama'ar kasashen biyu kwarai da gaske. A watan Maris na bana, a lokacin da shugaba XI Jinping ya kai ziyara a kasar Faransa, shugaba Macron ya je birnin Nice domin maraba da zuwan abokinsa Xi Jinping, inda suka kuma yi hira a wani kyakkyawan gidan dake kusa da teku har tsawon sa'o'i da dama. Kana, shugaba Macron ya mika wa shugaba Xi kyautar littafin "Bayani Kan Maganar Confucius" na harshen Faransanci da kansa. Shugaba Xi ya ce, lalle wannan kyauta ta zinariya ce. Sa'an nan, a watan Nuwamba na bana kuma, a lokacin da shugaba Macron ya kai ziyara a kasar Sin, ya zama shugaba na farko da ya halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, wato CIIE, cikin dukkanin shugabannin kasashen G7. Lamarin da ya nuna wa kasa da kasa dangantakar musamman dake tsakanin kasar Sin da kasar Faransa, cikin wannan zamani mai cike da canjawa.

A daren ranar 4 ga watan Nuwanba na shekarar 2019, shugaba Xi da uwargidansa sun kira liyafa a Otel din na Heping, domin maraba da zuwan bakin kasa da kasa, wadanda suka zo kasar Sin domin halartar bikin CIIE karo na biyu. Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya ce, "Cikin tarihin bunkasuwar kasar Sin, za a gane cewa, ci gaban duniya ya samar da ci gaban Sin, kana, ci gaban Sin zai tabbatar da babban ci gaban duniya. Ana cinikin hajoji a bikin CIIE, yayin da ake musayar ra'ayoyi da al'adu a bikin. Muna maraba da zuwan baki na kasa da kasa, kuma muna son kowa ya cimma moriya, domin biyan bukatun al'ummomin kasa da kasa na jin dadin zaman rayuwarsu."

Yayin bikin bude baje kolin CIIE, Xi Jinping ya ce, a nan muna da babbar kasuwa, muna kuma maraba ga kowa da kowa, ku zo ku gani. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China