Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan aikin nazarin kayayyakin tarihi da Sin take yi da hadin kai da ketare a bana ya kai 46
2019-12-24 10:56:41        cri

Hukuma mai kula da kayayyakin tarihi ta kasar Sin, ta kira taron hadin kan Sin da ketare kan ayyukan nazarin kayayyakin tarihi a jiya Litinin a nan birnin Beijing. Bayan taron an bayyana cewa, a shekarar nan ta 2019, ayyukan nazarin kayayyakin tarihi da Sin take gudanarwa da hadin kai da ketare da yawansu ya kai 46 suna shafar kasashe fiye da 20 dake nahiyoyin Asiya, Afrika, Turai da Amurka.

Ayyukan hadin kai a wannan fanni da Sin take gudanarwa, na nacewa ga tsarin musanyar al'adu karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya", kuma Sin ta kara hadin kanta da kasashen ketare, don nazari kayayyakin tarihi da gano gine-ginen tarihi, da bincike kan wasu manyan abubuwan tarihi, matakan da suka bayyana yadda mutanen da suka yin musanyar abubuwa, da kaurar mutane, da kuma hadewar tunani a kan hanyar siliki ta tarihi.

Ban da wanann kuma, aikin nazarin tabkin Bogoria na tarihi dake Kenya da kasashen biyu wato Sin da Kenya suke yi cikin hadin kai, da kuma aikin nazarin wurin ibada na MENTU na Luxor da Sin take yin hadin kai da Masar da dai sauransu, suna da alaka da asalin bil Adama, da al'adun zamanin da na duniya, da dai sauran abubuwa masu jan hankali a bangaren nazarin kayayyakin tarihi.

Sin na maraba da kwararrun ketare, wajen kawo ziyara kasar Sin, don hadin kai kan wannan aiki, lokacin da take kokarin fito da kan ta waje.

Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, yawan ayyukan da Sin ta gudanar da hadin kai da kasashe waje ya kai 46, wadanda suka shafi kasashe fiye da 20 daga nahiyoyin Asiya, da Afrika, Turai da Amurka. Kuma yawan hukumomin nazarin kimiyya da fasaha, da dakunan ajiye kayayyakin tarihi, da kuma jami'o'in da kasar Sin ta yi hadin kai da su a shekarar 2019 ya kai sama da 40. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China