Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin ya jaddada alfanun yarjejeniyar nukiliyar Iran a matsayin hanya mafi dacewa ta warware batun
2019-12-20 10:07:35        cri
Wakilin kasar Sin a MDD ya jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran a matsayin hanya mafi dacewa na warware batun nukiliyar kasar da kawo sassauci game da halin da ake ciki.

A lokacin taron kwamitin sulhun MDD game da hana bazuwar makaman nukiliya, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Zhang Jun, ya ce batun nukiliyar kasar Iran yana neman shiga wani matsanancin hali kuma aiwatar da yarjejeniyar yana gamuwa da tarin matsaloli.

Game da yanayin da ake ciki, jakadan na Sin ya bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa su yi aiki tare don sake farfado da tsarin daidaito da sauke nauyin dake bisa wuyansu karkashin yarjejeniyar, kasancewar yarjejeniyar tana da matukar muhimmanci wajen kawar da barazanar yaduwar makaman nukiliya a duniya, da tabbatar da zaman lafiyar kasa da kasa, da zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya.

Bugu da kari, wakilin na Sin ya bayyana damuwarsa game da matakin da Amurka ta dauka na ficewa daga yarjejeniyar da kuma daukar matakai na kashin kanta na kakabawa Iran takunkumi. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China