Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Labarin wani dan Najeriya dake kokarin cimma burinsa ta hanyar koyon yaren Sin
2019-12-16 14:09:39        cri

A kwanakin baya ne wani matashi dan asalin jihar Imon tarayyar Najeriya mai suna Samuel ya lashe gasar iya Sinanci bangaren Afirka wadda aka yi a kasar Sin, inda ya bayyana cewa, burinsa shi ne ta hanyar koyon Sinanci zai iya zama wani injiniyan kayan lataroni a nan gaba don ya taimaka ga samar da isasshen wutar lantarki a kasarsa.

Samuel, wanda ake kiransa Gu Siyuan a yaren Sin, dalibi ne dake wakiltar kwalejin Confucius ta jami'ar Nnamdi Azikiwe dake Najeriya wanda ya lashe gasar iya Sinanci da aka yi kwanakin baya a birnin Zhengzhou na kasar Sin, abin da ya ba shi damar samun kyautar kudin karatu a wata jami'ar kasar Sin don ya ci gaba da karo ilimi.

Labarin Gu Siyuan da yaren Sinanci ya samo asali ne daga wani makwabcinsa dake jihar Imon Najeriya. Gu Siyuan, ya kammala makarantar sakandare ne a shekara ta 2018, ya kuma yi tunanin ci gaba da karatu a kasar waje, inda makwabcinsa wanda ya taba koyon Sinanci a Kwalejin Confucius ya ba shi shawarar koyon yaren, saboda akwai yiwuwar zai samu damar yin karatu a kasar Sin ta hanyar koyon yaren, ta yadda zai iya cimma burinsa na zama injiniyan kayan lataroni don bada gudummawa ga warware matsalar rashin wutar lantarki wadda Najeriya ke fama da ita na dogon lokaci.

A nasa bangaren, jami'in kula da harkokin al'adu a ofishin jakadancin Sin dake Najeriya Li Xuda ya ce, yanzu akwai kwalejin Confucius guda biyu a fadin Najeriya, wadanda ke da dalibai sama da 2500 dake koyon Sinanci a ko wace shekara, inda a cewarsa, matasan Najeriya na da matukar sha'awar koyon yaren Sin, saboda idan ka koyi yaren na tsawon shekaru biyu ko uku, za ka iya samun gurbin aikin yi a wani kamfanin kasar Sin dake Najeriya har ma ka samu albashi mai kyau, kana kuma idan ka yi fice a fannin karatu, za ka iya samun damar ci gaba da karo ilimi a jami'o'in kasar Sin, abun dake jawo hankalin daliban Najeriya kwarai da gaske.

A watan Oktobar bara, Samuel ko kuma Gu Siyuan a yaren Sinanci, ya fara koyon Sinanci a kwalejin Confucius dake Jami'ar Nnamdi Azikiwe dake jihar Anambrar tarayyar Najeriya, inda ya nuna kaifin basirarsa wajen iya yaren. A watan Yunin bana kuma, Samuel wanda bai kai shekara daya yana koyon yaren Sinanci ba, ya ci mataki na hudu na jarrabawar iya Sinanci ko kuma HSK a takaice, har ma a watan Nuwamba ya ci mataki na biyar na jarrabawar bayan da ya halarci gasar iya Sinanci da aka gudanar a kasar Sin.

Malamin dake koyar da Samuel wato Zheng Jianle ya yaba sosai da koyon Sinanci da ya yi, inda ya ce, Samuel dalibi ne mai hikima, jajircewa da kuma son yin tunani da kansa, inda ya bada wani misalin cewa, a farkon zuwansa kasar Sin karatu, ya tambaye ni, a kan ce kaza da kifi su kan yi kwai a hausa, amma a yaren Sinanci, a kan ce kaza ta yi kwai amma kifi ya fitar da kwai maimakon ya yi kwai, to meye bambanci tsakanin kalmar yi da fitarwa a yaren Sin? Malam Zheng ya ce yana matukar mamakin ganin cewa, wani dalibin kasar waje wanda bai kai wata biyu ba yana koyon Sinanci zai yi irin wannan tambaya mai ma'ana.

Har wa yau, a yayin da yake halartar gasar iya Sinanci a kasar Sin, wani abu ya burge Samuel sosai. An tambayi mahalarta gasar ko suna da wasu abubuwa da za su yi a kasar Sin? Sun ce suna son dandana abincin Sin, ko zuwa yawon bude ido, ko kuma ganewa idanunsu al'adun gargajiya na kasar, amma amsar Samuel ita ce, yana son ya sayawa mahaifiyarsa keken dinki, saboda har yanzu tana amfani da keken dinki na shugabarta, inda furucinsa ya burge masu kallo sosai.

Sai dai bayan wasu kwanaki da Samuel yana dab da barin kasar Sin, wata malamar kasar Sin da ba su taba haduwa da juna ba ta je otel din Samuel har ta ba shi kudi, inda ta gaya masa cewa, zai yi wahala ta samu keken dinki a wurin, shi ya sa ta baiwa Samuel kudi don ya saya da kansa a Najeriya. Wannan abun kirkin da malamar ta yi ya burge Samuel kwarai da gaske, saboda bai taba tsammanin cewa wata bakuwa 'yar kasar Sin za ta maida hankali sosai kan irin wannan karamin burinsa ba, inda ya ce, zai yi amfani da wadannan kudade don ya saya wa mahaifiyarsa keken dinki, a kuma dauki hotonsa a turawa malamar. Saboda a cewar Samuel, abin da ya dace, shi ne ya ci gaba da yayata irin wannan kauna da kulawa da aka nuna masa zuwa ga mutanen da suke da bukata.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China