Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta yi kokarin ingiza neman cimma ra'ayin bai daya a tsakanin kasa da kasa yayin taron sauyin yanayi na Madrid
2019-12-13 14:07:34        cri

An kusan kammala taro karo na 25, na kasashen da suka sanya hannu kan tsarin yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD, kuma bangarorin daban-daban na shawarwari sosai tsakaninsu. Shugaban tawagar kasar Sin, kuma mataimakin hukumar kiyaye muhallin kasar Sin Zhao Yingmin, ya shaidawa manema labarai cewa, Sin za ta yi kokarin ingiza neman cimma ra'ayin bai daya a tsakanin kasa da kasa kan batun tinkarar sauyin yanayi.

Bangarori daban-daban sun kai ga cimma wani kunshin yarjejeniya kan matakan gudanar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, a gun taron sauyin yanayi da MDD ta gudanar a Katowice na kasar Poland a shekarar 2018, amma ba a kai ga cimma matsaya kan aya ta shida da ta shafi tsarin musanyar gurbatacciyar iska ta carbon-dioxide ba, inda aka ci gaba da tattauna batun a yayin taron na wannan karo.

A sa'i daya kuma, saboda karancin karfin siyasa, kasashe masu wadata ba su nuna himma da kwazo wajen taimakawa kasashe masu tasowa don tinkarar sauyin yanayi ba, wanda hakan ya sa bangarori daban-daban da wuya su kai ga cimma matsaya daya a shawarwarin. Game da hakan, shugaban tawagar kasar Sin, kuma mataimakin shugaban hukumar kiyaye muhallin halitun kasar Sin Zhao Yingmin ya bayyana matsaya uku da Sin take dauka kan wannan batu, ya ce:  

"Na farko, aya ta shida ta yarjejeniyar, wadda kamata ya yi ta kasance tsari da ya nuna daidaito, da adalci, kuma dake yin la'akari da moriyar bangarori daban-daban, ta yadda za a ba da tabbaci ga dora muhimmanci kan batutuwan dake jawo hankalin sassa daban-daban. Na biyu kuwa, kamata ya yi, a mai da hankali kan bukatar kasashe masu tasowa, musamman ma kudaden da suke bukata wajen tinkarar sauyin yanayi. Na uku, kaiwa ga ma'auni iri daya bisa tsarin yarjejeniyar Paris, don kaiwa ga matsaya wajen mayar da tsarin samun bunkasuwa da kiyaye muhalli na yarjejeniyar Kyoto zuwa ga tsarin na yarjejeniyar Paris."

An ba da labari cewa, a watan Nuwamban bana, Amurka ta sanar da janye jikinta daga yarjejeniyar Paris, saboda ganin haka, ko da yake bangarori daban-daban na da bambancin ra'ayi kan wasu batutuwa, amma sun kai ga matsaya kan yaki da manufar bangaranci, da manufar kariyar cinikayya, Zhao Yingmin ya ce:

"Manufar bangaranci da ta kariyar cinikayya, za su illata kwarin gwiwar kasashen duniya kan bunkasuwar kasa da kasa a nan gaba. Lamarin da zai kawo cikas ga kokarin da al'ummar duniya ke yi wajen tinkarar sauyin yanayi. Na tuntubi kusan duk ministoci na kasashe masu tasowa, har da wasu ministocin kasashe masu wadata, dukkanmu na ganin cewa, kamata ya yi mu yaki da wadannan manufofin biyu. Saboda kowa ya sani, ba zai yiwu ba a tinkari sauyin yanayi ta hanyar nuna bangaranci, abin da ake bukata shi ne hadin kai."

Shawarwarin sauyin yanayi ba ma kawai na da alaka da batun kimiyya ba, har ma na da babbar ma'ana ga bunkasuwar kasa da kasa a nan gaba. Saboda ganin hakan, a kan tattauna sosai, da yin ja-in-ja a taron sauyin yanayi na MDD a ko wace shekara. Sin ta kan samu amincewa daga kasashe daban-daban, saboda matsayin da take dauka a taron. Hakan ya sa, bisa rokon shugaban taron, Sin ta dauki nauyin dake wuyanta na daidaitawa, da yin sulhu kan matsayin bangarorin daban-daban. Zhao ya kara da cewa, ko da yake akwai bambancin ra'ayi, amma Sin za ta yi kokarin sa kaimi ga cimma matsaya a tsakanin bangarori daban daban don tinkarar sauyin yanayi. Ya ce:  

"A hakika dai, tinkarar sauyin yanayi aiki ne mai matukar wuya, amma hakan ba ya nufin cewa, ba za a iya warware matsalar ba. Ko wace kasa tana da nata muradu kan batun sauyin yanayi, wannan ba abin mamaki ba ne, idan mun tsaya kan manufar gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam, to, na yi imanin cewa, za mu iya cimma matsaya kan wasu muhimman batutuwa a yayin taron." (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China