Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dole ne a yi adawa da ra'ayin bangaranci da ba da kariya
2019-12-12 18:59:55        cri

Yau gidan rediyon kasar Sin ya fitar da wani sharhi mai taken "Dole ne a yi adawa da ra'ayin bangaranci da ba da kariya musamman ma yayin da kungiyar cinikayyar duniya ke fuskantar rikici", inda aka bayyana cewa, kotun sauraron kara ta kungiyar cinikayyar duniya ta daina zaman sauraron kara jiya saboda Amurka ta hana a yi zabi da kuma nada sabon alkalin kotun, lamarin da ake dauka a matsayin kalubale mafi tsanani da tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban ke fuskanta.

Sharhin ya kara da cewa, matakin da Amurka ta dauka ya kawo babbar illa ga kungiyar cinikayyar duniya, hakan ya nuna cewa, kungiyar tana gudanar da aikinta ne karkashin jagorancin Amurka, a don haka dole ne a gaggauta yin gyara da kuma kyautata tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban da ake amfani da shi yanzu. Kana sharhin ya jaddada cewa, kasar Sin tana goyon bayan gudanar da cinikayya cikin 'yanci, kuma tana goyon bayan tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban da aka tsara bisa adalci, haka kuma tana ganin cewa, ya kamata a yiwa tsarin tafiyar da kungiyar cinikayyar duniya kwaskwarima, saboda ya dace a bullo da ka'idojin yin hakurin juna da rashin nuna wariya da kuma bude kofa, ta yadda za a tabbatar da moriyar ci gaban kasashe masu tasowa.

Yanzu abu mafi muhimamnci shi ne kungiyar cinikayyar duniya ta fara gudanar da aikin zabin alkalan kotun sauraron kararta nan da nan, kana ya kamata daukacin kasashen duniya su hada kai don nuna adawa da ra'ayin bangaranci da ba da kariya domin kare kima da amfanin kungiyar cinikayyar duniya, tare kuma da samun ci gaba tare.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China