Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban jihar Xinjiang: Ko kadan ba wanda zai hana bunkasuwar jihar
2019-12-11 14:29:20        cri

Kwanan baya, mataimakin direktan kwamitin JKS reshen jihar Xinjiang, kana shugaban gwamnatin jihar Shohrat Zakir, ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, majalisar wakilan Amurka ta zartas da doka, wato wai dokar hakkin Bil Adama na Uygur na shekarar 2019, abun da ya keta dokar kasa da kasa, da ka'ida mai tushe ta dangantakar kasa da kasa, wanda hakan shisshigi ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Ya kuma jaddada cewa, ba wanda zai hana bunkasuwar jihar mai wadata, da kuma hadin gwiwar al'umomin jihar.

Masu sauraro, abokiyar aikinmu Amina Xu ta nazarci wannan batu, ga cikakken bayani da ta hadda mana.

Mataimakin direktan kwamitin JKS reshen jihar Xinjiang, kana shugaban gwamnatin jihar, Shohrat Zakir, ya bayyana a gun taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya cewa, jihar Xinjiang tamkar wani lu'u lu'u ne mai haske dake yammacin kasar Sin, kuma muhimmin mataki ne cikin shawarar "Ziri daya da hanya daya", kana kuma kasar ta fidda jerin manufofi na musamman don goyon bayan bunkasuwar tattalin arziki da al'ummar jihar. Kazalika, hukumar harkar kudi ta gwamnatin tsakiyar kasar Sin tana baiwa jihar tallafin kudi RMB Yuan biliyan 400 a kowace shekara, haka kuma larduna da birane 19 sun dade suna taimakawa harkokin jihar. Yawan kudin da aka zuba a jihar ya kai fiye da RMB Yuan biliyan 15 a kowace shekara. Hakan ya sa, mazauna Xinjiang na zaman rayuwa mai inganci, da samun bunkasuwar tattalin arziki da hadewar al'umomi. Ban da wannan kuma, addinai na zaman tare cikin jituwa, da samun kyautatuwar rayuwar jama'a da gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Ya ce:

"Zaman karko mai jituwa na da matukar wuyar samu a jihar, saboda an dade ana fama da ta'addanci, lamarin da ya keta hakkin rayuwa da samun bunkasuwar al'ummar jihar. Muna nacewa ga gudanar da harkoki bisa doka karkashin tsarin mulki na gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, don yaki da ta'addanci bisa doka. A sa'i daya kuma, mun mai da hankali kan kawar da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi daga tushe, wato kyautata rayuwar jama'a, da inganta aikin ba da ilmin doka, da kafa cibiyoyin horar da sana'o'i, matakan da suka aza tubali mai inganci ga zaman karko da jituwa cikin dogon lokaci a jihar. Har ila yau, jihar ba ta samu ayyukan ta'addanci a shekaru 3 a jere da suka gabata ba, kana al'umomi daban-daban na rayuwa cikin annashuwa."

Ban da wannan kuma, Shohrat Zakir ya ce, tattalin arzikin jihar na bunkasuwa yadda ya kamata shekarun baya-bayan nan. Tun bayan da aka kira taron kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, saurin bunkasuwar GPDn jihar ya kai kashi 8.5 cikin dari a ko wace shekara, kana yawan kudin shiga na mazaunan birane da kauyukan ya karu da kashi 8.4 cikin dari da kashi 8.2 cikin dari. Kaza lika yawan masu bude ido da jihar ta karba a shekarar 2018 ya kai miliyan 150, wanda ya karu da kashi 40.1 cikin dari bisa na shekarar 2017. Ban da wannan kuma, wannan adadi ya kai fiye da miliyan 200 a watanni 10 da suka gabata bana, wanda ya karu da kashi 42.6 cikin dari bisa na bara. Hakazalika, an kubutar da mutane fiye da miliyan 2.38 daga kangin talauci tun daga shekarar 2014, matakin da ya sa yawan matalauta ya ragu daga kashi 22.84 cikin dari a shekarar 2014 zuwa kashi 6.51 cikin dari a bana.

Kwanan baya, majalisar wakilan Amurka ta zartas da wata doka wai "Dokar hakkin Bil Adama na Uygur na shekarar 2019", wadda ta shafi kashin kaji kan aikin yaki da ta'addanci da ake gudana a jihar. Shohrat Zakir ya ce, Amurka ta nuna halin ko in kula kan barazanar ta'addanci da jihar ke fuskanta, amma yanzu tana fakewa da wannan batu, bisa ganin yadda jihar ta yi rayuwa mai annashuwa da zama cikin wadata da jituwa don talaka dangantakar al'umomoin kasar Sin. Ya ce:

"Shisshigi ne cikin harkokin cikin gidan kasarmu, wanda ya keta dokar kasa da kasa, da ka'idar dangantakar kasa da kasa. Matakan da Xinjiang ke dauka na yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi, iri daya ne da wadanda sauran kasashe a duniya ke dauka, ciki hadda Amurka. Kamata ya yi, wasu Amurkawa sun yi watsi da bambancin ra'ayi, da fuska biyu da suke da ita kan aikin yaki da ta'addanci, da kawar da tsattsauran ra'ayi, domin ba wanda zai hana bunkasuwar jihar Xinjiang."

Zaunannen mamban kwamitin reshen jihar Xinjiang ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin shugaban gwamnatin jihar Arkin Turniyaz ya nuna cewa, al'umomin jihar na fahimtar cewa, halin karko ya fi tarzoma, hakan ya sa mazauna wurin ke dukufa kan tabbatar da zaman karko a jihar, kuma ba wani karfin ketare da zai iya canja zukatansu a wannan fanni. Ya ce:

"Babu wata kasa da ba ta bukatar halin karko a gida da waje don samun bunkasuwa, wadannan matakai biyu na dogaro ne da juna. Idan babu tabbacin zaman karko a al'umma, to kuwa ci gaban da aka riga aka samu ma zai baci."

Game da cibiyoyin koyon ilmin sana'o'i da ake aiwatarwa a jihar, wadanda suke jawo hankalin mutane sosai, Shohrat Zakir ya yi bayani cewa:  

"Saboda ganin ta'addanci mai tsanani da jihar ke fuskanta, mun kafa wadannan cibiyoyi. Wasu sun kammala karatu sun koma gida, sun samu aikin yi, kuma akwai sabbin dalibai da suka shiga. Ya zuwa yanzu, Dukkan daliban da suka koyi Sinanci da ilmin doka da shari'a, da fasahohin sana'o'i, sun kammala karatunsu, kuma sun samu guraben aikin yi bisa taimakon hukumomin gwamnati. Matakin da ya kyautata rayuwarsu matuka. Abin da ya shaida cewa, wadannan cibiyoyyi sun kasance matakin da ya dace, wajen kokarin samun nasarar yakar ta'addanci, da kawar da tsattsauran ra'ayi."

Ya kara da cewa, idan ana bukata, kowa na iya shiga wadannan cibiyoyi don kara ilmi bisa zukatansu kamar yadda suke fata. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China