2019-12-09 14:44:51 cri |
Yau za mu yi muku bayani kan kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi domin samar da tsaron hatsi ga al'ummarta.
A ranar 14 ga watan Oktoban shekarar 2019, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani mai taken "tsaron hatsin kasar Sin", wannan shi ne karo na biyu da ya fitar da takardar bayanin tun bayan shekarar 1996, inda aka yi nuni da cewa, tun bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin shekaru 70 da suka gabata wato a shekarar 1949, kasar Sin ta samu babban sakamakon da ya jawo hankalin al'ummun kasashen duniya a bangaren samar da tsaron hatsi, haka kuma tana kara bude kasuwar hatsinta ga kasashen ketare, domin ingiza ci gaban cinikin hatsi tsakanin kasa da kasa, tare kuma da kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen duniya a fannin samar da hatsi, ta yadda za a cimma burin kiyaye tsaron hatsi a fadin duniya.(Jamila)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China