Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamata ya yi kasar Amurka ta kauracewa kawo cikas ga aikin yaki da ta'addanci na kasa da kasa
2019-12-06 19:49:17        cri
Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ya ba da sharhi a yau Juma'a mai taken "Gargadi ga kasar Amurka da ta kauracewa kawo cikas ga aikin yaki da ta'addanci na kasa da kasa".

Sharhin ya ce, kwanan baya kasar Amurka ta zartas da dokar hakkin bil Adama game da yankin Xinjiang na Uygur na shekarar 2019, inda ta bata sunan kasar Sin kan kokarinta na yaki da ta'addanci da ra'ayin 'yan aware, kana ta fatattaki manufofin gwamnatin kasar Sin kan gudanar da harkokin yankin Xinjiang, matakin da ya keta dokokin kasa da kasa.

Dokar ta bayyana yadda kasar Amurka ke nuna rashin gaskiya da adalci kan batun yaki da ta'addanci, da nufinta na amfani da batun hakkin bil Adama, don tsoma baki cikin harkokin gidan kasar ta Sin, wadda ta isar da sako na kuskure ga masu ta'addanci, a hannu guda kuma ta gamu da adawa daga bangaren jama'ar kasar Sin da kasashen duniya.

Sharhin ya jaddada cewa, batun Xinjiang, ba batun ne da ya shafi hakkin bil Adama, ko kabilu da kuma addinai ba, a maimakon haka yana da alaka ne da aikin yaki da ta'addanci da ra'ayin 'yan aware. Don haka ana gargadi ga kasar Amurka, da ta dakatar da mugun aikinta na tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin kiri da muzu ta hanyar amfani da batun Xinjiang, da yin watsi da ra'ayinta na rashin gaskiya da adalci, kuma a maimakon kawo cikas ga aiki na yaki da ta'addanci na kasa da kasa, ta samar da taimakonta ta fannin. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China