Kamar yadda Bahaushe kan ce, a nemi ilmi ko a birnin Sin ne. A yayin da hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ke dada bunkasa ta fannoni daban daban, karin matasa 'yan Afirka na zuwa nan kasar Sin domin karo ilmi, kuma Ibrahim Aliyu, wanda ya fito daga tarayyar Nijeriya na daya daga cikinsu. To, shin yaya yake gudanar da harkokinsa na karatu a nan kasar Sin? Ku biyo mu cikin shirin, don jin yadda Ibrahim Aliyu yake rayuwa a kasar Sin cikin tattaunawarsu da Lubabatu.