Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron sauyin yanayi na MDD na 2019 a Madrid
2019-12-03 14:47:27        cri


An bude taron kasashen da suka sa hannu kan yarjejeniyar tsarin sauyin yanayi na MDD karo na 25 na shekarar 2019 a Madrid na kasar Spaniya a jiya Litinin. Abin da aka sa gaba a wannan karo shi ne, yin tattaunawa kan batutuwan da suka rage game da aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris. Tawagar Sin a taron ta nuna cewa, kamata ya yi, bangarori daban-daban su dauki matakan da suka dace wajen tinkarar sauyin yanayi.

Da safiyar ran 2 ga wata agogon wuri, aka bude taron kasashen da suka sa hannu kan yarjejeniyar tsarin sauyin yanayi na MDD karo na 25 na shekarar 2019 a cibiyar baje koli ta Madrid.

Kafin bude taron, bangarori daban-daban sun ba da jerin rahotanni ciki hadda kungiyar binciken yanayin sararin samaniya ta duniya da hukumar kiyaye muhalli ta MDD wato UNEP da sauransu, don nanata mumunan sakamakon sauyin yanayi. Babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya yi jawabi a wajen bude taron, inda ya gargadi bangarori daban-daban cewa, tinkarar sauyin yanayi batu ne da kamata ya yi a warware shi ba tare da bata lokaci ba, ya ce:

"Kungiyar binciken yanayin sararin samaniya ta duniya ta gabatar da alkaluma cewa, iska mai gurbata muhalli da aka fitar ya kai wani sabon matsayi. Inda matsakaicin yawan iskar cabon dioxide da aka fitar ta kai kashi 407.9 cikin miliyan daya a shekarar 2018, amma a baya, ba da dadewa ba, ana ganin cewa da kyar za a iya kaiwa kashi 400 cikin miliyan daya. Shekaru 5 da suka gabata, shekaru ne mafi zafi a tarihi, mumunan sakamakon da ya haifar sun hadda da mahaukaciyar guguwa, da tsananin fari da ambaliyar ruwa da gobarar gandun daji da sauransu. Ban da wannan kuma, leburin teku na kara dagawa saboda narkewar kankara."

Taron a wannan karo ya kasance na karshe kafin an fara aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris a dukkan fannoni na shekarar 2020. A gun taro karo na 24, bangarori daban-daban sun kai ga matsaya daya kan yawancin matakan gudanarwa, amma abubuwan dake da nasaba da iskar cabon dioxide da suka rage ga taro a wannan karo, ya fi ba mahalarta wahala, ya ce:

"Abokai mahalarta taron, mun hadu mu yi taro a wannan karo don samun ci gaba kan aya ta 6 ta yarjejeniyar Paris, wadda ba a warware ta a taron da ya gabata a Poland ba. Muna fatan hana karuwar yawan zafin duniya, don kaucewa sauyin yanayi da ba za a iya sarrafawa ba, muhimmin aiki shi ne tabbatar da farashin iskar cabon dioxide. Aiwatar da aya ta 6 za ta taimaka wajen gudanar da kasuwar iskar cabon dioxide, da sa kaimi kan sassa masu zaman kansu da kuma tabbatar da ka'ida iri daya ga kowa. Idan ba haka ba, kasuwar za ta tabarbare tare da samar da sakamako mara kyau, har ta kawo cikas ga kokarin da muke yi wajen tinkarar sauyin yanayi. Ina kalubalantar bangarori daban-daban da su daidaita bambancin ra'ayinsu don kai wa ga matsaya daya kan wannan batu."

A wannan rana kuma, mataimakin sakataren tawagar Sin a taron, kuma mataimakin shugaban sashen kula da yanayi na ma'aikatar muhalli ta kasar Sin, Lu Xinming ya shedawa manema labarai cewa, tawagar za ta ba da gudummawa wajen ingiza yin tattaunawa kan yarjejeniyar Paris musamman ma aya ta 6 da ta rage. Ya ce, Sin na fatan samun ci gaba kan batun kudi da tabbatar da alkawarin kasa da kasa kafin shekarar 2020, ya ce:

"Muna fatan za a samu ci gaba kan batun kudi, saboda ana bukatar kudi wajen aiwatar da ayyuka da tabbatar da muradu, kuma muna fatan kasashe masu wadata za su baiwa kasashe masu tasowa karin kudi kyauta a wannan fanni. Ban da wanann kuma, muna fatan a bada tabbaci ga alkawarin da kasa da kasa suka yi, musamman ma cike gibin alkawari da na kudi da kasashe masu wadata da mafi karfin masana'antu suka yi kan rage fitar da gurbatacciyar iska, kafin shekarar 2020."

Kungiyar hadin kai da raya tattalin arziki ta kasa da kasa mai mambobin kasashe masu ci gaba, ta ba da rahoto a kwanakin baya cewa, kashi 20 cikin dari na kudin kwamitin tallafawa mambobin kungiyar kawai aka yi amfani da shi, wajen tinkarar sauyin yanayi. Rahoton na nuna cewa, kamata ya yi mambobin kasashe su samar da karin kudade a wannan fanni.

Lu Xinming ya ce, abu mafi muhimmanci da aka sa a gaba shi ne hadin kan kasa da kasa don daukar matakan da suka dace wajen tinkarar sauyin yanayi, ya ce, tilas ne su warware matsalar dake gabansu yanzu, wato rage fitar da gurbataciyyar iska kafin shekarar 2020. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China