Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin Na Kokarin Kasancewa Kasa Mai Karfin Cinikayya
2019-12-03 14:42:59        cri
A kwanakin baya, Sin ta gabatar da shawarwari kan yadda za a sa kaimi ga samun ci gaban cinikayya mai inganci, don tsara taswirar inganta cinikayyar kasar Sin mai inganci, da sa kaimi ga kasar Sin ta yadda za ta kasance kasar dake kan gaba a fannin cinikayya a duniya.

Wadannan matakai za su kyautata tsarin cinikayya na kasar Sin, da kara nuna goyon baya ga ciniki a tsakanin kasa da kasa ta yanar gizo, da cinikin bada hidima da sauransu. Kana a matsayinta na kasa dake wakiltar kasashe masu tasowa, kasar Sin za ta shiga aikin tsara ka'idojin cinikin duniya, hakan zai kyautata tsarin ciniki cikin adalci.

Abin da kasar Sin ta ke bukata don samun ci gaban ciniki, shi ne ci gaban tattalin arziki mai inganci. Idan kasar Sin ta samu bunkasuwa mai dorewa a fannonin ciniki da tattalin arziki, hakan zai bada gudummawa ga raya tattalin arzikin duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China