Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A gaggauta raya yankin delta na kogin Yangtze har ya zama muhimmin wuri na bude kofar kasar Sin ga kasashen waje
2019-12-02 20:48:11        cri
Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a taikace, ya fitar da sharhi a yau Litinin, mai taken "A gaggauta raya yankin delta na kogin Yangtze, don ya zama sabon wuri na bude kofar kasar Sin ga kasashen waje".

A cewar sharhin, a kwanakin baya, kasar Sin ta bullo da wata muhimmiyar takarda kan shirin raya yankin delta na kogin Yangtze na bai daya, inda aka tsara manufofin bunkasa birnin Shanghai, da lardunan Jiangsu, da Zhejiang da kuma Anhui nan da shekaru biyar, zuwa goma sha biyar dake tafe. Sharhin ya ce yankin delta na kogin Yangtze zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa, wajen habaka tattalin arzikin kasar Sin.

Kaza lika sharhin ya yi nuni da cewa, a nan gaba yankin delta na kogin Yangtze, zai zama muhimmin wurin gwaji na aiwatar da manufar kasar Sin ta bude kofarta ga kasashen ketare a sabon zagaye, da ci gaba da inganta aikin zuba jari da hadin-gwiwa tsakanin Sin da kasashen waje, da zama kyakkyawan abun misali ga aikin samar da yanayin kasuwanci mai kyau.

Har wa yau, sharhin ya ce, kasa da kasa za su iya fahimtar niyyar gwamnatin kasar Sin ta habaka bude kofa ga kasashen waje, ta yadda za su iya more damar ci gaban tattalin arzikin kasar. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China