Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU: Zaben Namibiya ya dace da dokokin kasar har ma da tsarin kasa da kasa
2019-12-02 11:02:12        cri

Tawagar kungiyar tarayyar Afrika AU dake sa ido a babban zaben kasar Namibiya wato (AUEOM), ta sanar cewa, an gudanar da zabuka bisa tsarin dokokin kasar Namibiya kuma ya yi daidai da matakin kasa da kasa.

A sanarwar da tawagar AUEOM ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ta taya gwamnati da jama'ar kasar Namibiya murnar kammala gudanar da babban zaben kasar cikin kwanciyar hankali.

Sanarwar ta ce, bisa ga irin abubuwan da suka faru, AUEOM ta tabbatar da cewa, babban zaben na ranar 27 ga watan Nuwamba an gudanar da shi bisa dokokin kasar kuma ya yi daidai da tsarin kasa da kasa. Zaben ya baiwa jama'ar kasar Namibiya damar bayyana ra'ayinsu cikin 'yanci da walwala.

AUEOM ta kuma yabawa gwamnatin kasar Namibiya sakamakon rattaba hannu da ta yi kan dokokin tsarin demokuradiyyar Afrika, da tsarin zabuka, da kuma shugabanci, wanda mambobin kasashen Afrika 55 suka amince da shi bayan babban zaben shekarar 2014.

Tawagar sa ido a zaben ta ziyarci rumfunan zabe kimanin 107 inda suka sanya ido tun daga lokacin bude rumfunan zaben, zuwa lokacin kada kuri'u, da rufa rumfuna tare da kidaya kuri'un, daga cikin yankunan da ta ziyarta, kashi 75 daga yankunan biranen kasar ne sai kuma ragowar a yankunan karkara.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China