Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me ka sani game da ranar cutar Kanjamau
2019-12-01 16:14:52        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO ce ta kebe ranar 1 ga watan Disamban kowacce shekara, a matsayin ranar Cutar Kanjamu ta duniya, tun daga shekarar 1988, domin wayar da kan jama'a game da cutar.

A cewar shirin yaki da cutar ta MDD, UNAIDS, Taken ranar a bana shi ne "al'ummomi su samar da sauyi", wanda ke bayyana rawar da al'ummomi za su iya takawa wajen daukar matakan kariya da kulawa da kuma taimakawa mutane masu dauke da cutar.

Bisa alkaluman da WHO ta fitar, ya zuwa karshen shekarar 2018, akwai mutane miliyan 37.9 dake rayuwa da cutar kanjamau a fadin duniya. Sannan sama da kaso 2 bisa 3n masu dauke da cutar na nahiyar Afrika, musamman kasashen dake kudu da hamadar sahara.

A yanzu, kasar Sin ce ke shugabantar hukumar gudanarwar shirin UNAIDS, wadda ke jagorantar ayyukan Shirin, mai wakilai daga gwamnatocin kasashe 22.

Kasar Sin ta kulla kyakkyawar dangantaka da Tarayyar Afrika, inda take samar da taimako, ciki har da horar da kwararrun dake taka muhimmiyar rawa wajen yaki cutar da kuma tura ayarin jami'an lafiya zuwa yankunan Afrika da suka fi fama da cutar.

Ko a watan Satumban 2018, yayin taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika, an ayyana kiwon lafiyar al'umma a matsayin daya daga cikin manyan bangarorin hadin gwiwar Sin da Afrika a fannin kiwon lafiya.

Gabanin ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya karo na 32 a yau Lahadi, Firaministan kasar Sin, Li Keqiang, ya yi kira da kada a yi kasa a gwiwa a kokarin daukar matakan kariya da yaki da cutuka masu yaduwa kamar ta kanjamau. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China