Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunonin sojin ruwan kasashen Afirka ta kudu da Rasha da Sin sun yi atisaye a teku tare
2019-12-02 07:47:32        cri

Dakarun rundunar sojojin ruwan Afirka ta kudu, suna yin atisaye a teku tare da takwarorin su na kasahen Rasha da Sin, a yankin tekun kudancin kasar dake daura da birnin Cape Town. Wannan ne karon farko da kasashen uku suka yi atisayen sojin ruwa a tarihi.

Yayin atisayen da ya gudana tsakanin ranakun 25 zuwa 30 ga watan Nuwambar nan, sojojin sun maida hankali ga ayyukan samar da tsaro ga sashen tattalin arzikin teku, da aikin hadin gwiwa, da tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin dakarun da suka halarci atisayen. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China