Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta karbi ragamar shugabancin kungiyar raya yankin gabashin Afrika (IGAD)
2019-11-30 15:43:10        cri
An kammala babban taro karo na 13 na kungiyar raya yankin gabashin Afrika IGAD, a jiya Juma'a a birnin Addis Ababa na Habasha, inda Sudan ta karbi ragamar shugabancin kungiyar.

Kungiyar kasashe 8, mai kokarin raya harkokin cinikayya da tsaro a yankin gabashin Afrika, ta zabi kasar Sudan ta maye gurbin Habasha, a matsayin shugabar kungiyar, inda ake sa ran Sudan din ta rike mukamin tsawon shekara guda.

Firaministan Sudan, Abdalla Hamdok ya karbi mukamin daga hannun takwaransa na Habasha, Abiy Ahmed, yayin wani bikin da ya gudana a karshen taron kungiyar IGAD karo na 13.

IGAD ta kasance mai shiga tsakani a kokarinta na kawo karshen yakin basasar Sudan ta kudu, tun bayan da rikici ya barke a kasar mafi kankantar shekaru a duniya a watan Disamban 2013.

Haka zalika, kasashe mambobin IGAD, sun kasance mafi bayar da gudunmuwar dakaru ga shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika a Somalia, wanda aka dorawa alhakin tabbatar da zaman lafiya da kawo karshen barazanar kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta al-Shabab a Somalia.

Taron na IGAD, ya kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi tsattsauran ra'ayi da gurbatar yanayi da fashin teku da bakin haure da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin 'yanci a tekun Bahar Maliya da Gabar Tekun Aden. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China