Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala aikin ginshikan ginin majalisar dokokin Zimbabwe da Sin ta tallafawa gina shi
2019-11-29 14:58:36        cri

Ginin majalisar dokokin Zimbabwe aiki ne mafi girma da Sin take taimakawa gudanarwa a kudancin Afrika. Lokacin da aka kusa kammala aikin ginshikan ginin, shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya kai ziyarar wurin, tare da godewa taimako da goyon bayan da Sin ta dade tana baiwa kasarsa.

Ranar 27 ga wata agogon wurin, shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da mataimakansa, Constantino Chiwenga da Kembo Mohadi da kuma wasu manyan jami'an gwamnatin kasar, sun kai ziyara wurin aikin wannan gini, inda Mnangagwa ya jinjinawa aikin da aka gudanar a tsanake, tare da yabawa Sin bisa gudanar da shi cikin sauri, wanda ya amfanawa jama'a kwarai da gaske. Ya ce:

"Wannan ne karo na uku da na ziyarci wurin aikin, wanda aiki ne dake da muhimmanci sosai ga al'ummar kasar, Sin ta taimaka mana wajen yin wannan ginin na zamani, ina godiya matuka. Muna ganin cewa, kamata ya yi kasar ta nemi taimako daga ketare yayin da take kokarin samun bunkasuwarta da zamanintar da masana'antu. Hakan ya sa, nake farin ciki sosai da ganin an samun ci gaba mai kyau kan wannan gini, har ma ina mamaki sosai kan babban sauyin da ake samu a ko wane karo, kamfanin SCG dake daukar nauyin ginin da ma'aikatan wurin, sun hada kan cimma wannan ci gaba ne cikin gajere lokaci."

Wannan gini na zaune ne a sabon birnin dake tudun Hampton mai nisan kilomita 20 yamma da Harare, fadar mulkin kasar, an fara wannan aiki a ran 30 ga watan Nuwamba na shekarar 2018, ana sa ran kammala aikin gina ginshikansa a ranar 30 ga watan nan, wannan babban gini zai zama wata alama ta Zimbabwe. Mukaddashin wakilin Sin dake Zimbabwe Zhao Baogang ya yi bayanin cewa:

"Wannan gini ya zama irinsa mafi girma da Sin ta taimaka wajen ginawa a wata kasa na Afrika a shekarun nan na baya-baya, wanda girmansa ya kai muraba'in mita dubu 33 dake kunshe da hawa 6 da manyan dakunan taro 2 da dai ragowar na'urori. Bisa kwangilar da aka kulla, za a kammala wannan aiki cikin watanni 32, wato za a mika shi ga Zimbawe kafin watan Maris na shekarar 2021. Ya zuwa yanzu dai, an tafiyar da aikin yadda ya kamata, kuma ana cimma nasarar gina ginshinkansa, wanda ya zama wani muhimmin mataki cikin wannan aiki gaba daya. Na yi imanin cewa, bisa kokarin da ma'aikatan Sin da Zimbabwe suke yi, za a kammala wannan aiki cikin lokaci, matakin da zai zama wani ci gaba mai armashi na hadin kan kasashen biyu."

An ba da labari cewa, ma'aikata Sinawa fiye da 160 ne ke cikin wannan aiki, kuma aikin ya samar da guraben aikin yi sama da 800 ga mazauna wurin. Ban da wannan kuma, an sayi kayayyakin da ake amfani da su a aiki daga wurin, kamar su rairayi, kananan duwatsu, siminti da sauransu, matakin da ya ingiza bunkasuwar kasuwar kayayyakin gine-gine a wurin.

Ban da wannan gini kuma, Sin ta taimaka wajen gina wasu ayyuka da dama a Zimbabwe, matakan da suka kyautata manyan ababen more rayuwar jama'ar kasar, da kuma sassauta halin karancin makamashi ciki hadda wutar lantarki da kasar ke fuskanta. A cikin jawabin da shugaba Mnangagwa ya bayar, ya ambaci ayyukan hadin kan kasashen biyu da dama, a cewarsa, Sin sahihiyar kawa ce ga Zimababawe. Ya ce:

"Shekarar bara, yayin da na kai ziyara ta biyu a kasar Sin, mun daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa dangantakar abota ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, matakin da ya kara dankon zumuncin kasashen biyu. A Sa'i daya kuma, Sin ta samarwa kasar damammaki masu dimbin yawa na hadin kai, ban da wannan ginin, kamfannin Sin na sauke nauyin dake wuyansa kan aikin habaka filin saukar jiragen sama na Victoria Falls, aikin habaka tashar samar da wutar lantarki da karfin ruwa na kudancin gabar Kariba, da aikin habaka na'urorin samar da wutar lantarki ta karfin wuta mai lamba 7 da 8 na Hwange da dai sauransu, ya zuwa yanzu dai, Sin ta ba da rancen kudi ga aikin habaka filin saukar jiragen sama na birnin Harare. Akwai irin wadannan ayyuka da dama, wasu an kammala su, wasu ana gudanar da su. Gwamnatin kasar da jam'iyyun kasar da kuma jama'ar kasar na matukar godiya ga taimakon da Sin take ba mu, abin da ya shaida zumunci na kut da kut tsakaninmu." (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China