Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ramos Na Son Komawa Kasar Sin Da Buga Wasa
2019-12-05 16:02:14        cri

Na Samu Babbar Kungiya A Duniya, Cewar Mourinho

Sabon mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Jose Mourinho, ya bayyana cewa, ya yi farin cikin samun akin koyarwar kungiyar, domin ya samu babbar kungiyar kwallon kafa a duniya, wacce ta ke da tarihi da burin samun nasara. Dan kasar Portugal din, Mourinho ya maye gurbin dan kasar Argentina, Maurico Pochentino da kungiyar kwallon kafar Tottenham ta yi waje da shi a daren ranar Talata sakamakon rashin samun nasara. A sanarwar da kungiyar ta Tottenham ta fitar,cimma wannan yarjejeniya da Mourinho na da nasaba da irin rawar da ya taka a baya kasancewa ya taba horar da kungiyoyi da suka hada da Chelsea da Manchester United a gasar firimiya ta Ingila. Sanarwar da kungiyar ta gabatar ta ce Mourinho wanda tsohon mai horar da kungiyoyin Chelsea da Manchester United da Real Madrid ne, ya sanya hannu kan kwangilar da zata kai shi zuwa karshen kakar shekarar 2022 zuwa 2023 wato shekara uku da rabi. Shi dai Pochettino mai shekaru 47 a duniya ya fara aiki ne da Tottenham Hotspur a shekarar 2014 bayan ya bar kungiyar Southampton, inda ya sauya alkiblar kungiyar ta zama daya daga cikin wadanda ake tinkaho da su a Ingila da kuma gasar cin kofin zakarun Turai, inda suka kai matakin karshe a karon farko a kakar data gabata. Matsalolin da kungiyar ta samu a kakar bana wanda ya bar ta a matsayi na 14 a teburin firimiya da kuma samun maki 3 kacal daga wasanni 12 da ta buga, ya harzuka shugabannin kungiyar da magoya bayan ta. Tuni dai aka fitar da kungiyar Tottenham daga gasar League Cup yayin da Bayern Munnich ta yiwa kungiyar cin kaca daci 7-2 a gasar cin kofin zakarun Turai wanda sakamakon ma ya sake tunzura shugaban kungiyar, Daniel Leby. Tuni Mourinho ya bayyana farin cikin sa da nadin da akai masa, inda ya bayyana gamsuwa da zaratan 'yan wasan dake kungiyar da kuma bangaren yaran da ake horar wa kuma yayi alkawarin zai dawo da martabar Tottenham din.

Luis Enrique Ya Sake Zama Kociyan Sipaniya

Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Luis Enrique, zai cigaba da horar da tawagar kungiyar kwallon kafar kasar Sifaniya, bayan wata biyar kenan da kocin ya ajiye aikinsa. Enrique ya ajiye aiki a watan Yuni bayan ya yi wata biyar yana jan ragamar kungiyar, sai dai a watan Agusta ya sanar da mutuwar diyarsa 'yar shekara tara mai suna Dana, sakamakon ciwon daji. Tsohon kocin na Barcelona mai shekara 49 an maye gurbinsa da mataimakinsa, Robert Moreno kuma Moreno na rike da ragamar kungiyar kwallon kafar Sifaniya lokacin da kasar ta doke Romania da ci 5-0. Hakan ya sanya Sipaniya ta kammala wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Euro 2020 ba tare da an doke ta ba wanda kuma hakan yasa yanzu kasar ta shirya tsaf domin tunkarar wasannin gasar a shekara mai kamawa. Moreno, wanda shi ma ya yi aiki karkashin Enrikue a Roma, Celta Bigo da Barcelona, ya ce zai ajiye mukamin a duk lokacin da Enrikue din ya bukaci dawowa kuma a wani taron manema labarai ranar Talata, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Sifaniya, Luis Rubiales ya ce Kowa ya sani cewa idan Luis Enrikue yana son dawowa to kofa a bude take. Ya ce Luis Enrique zai ci gaba da rike ragamar kungiyar har zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Katar a shekara ta 2022 saboda yana fatan alheri da fatan kuma zai dawo da karsashi da kuma shirin gasar turai ta badi An nada Enrique a matsayin mai horar da 'yan kwallon kasar bayan ficewar Sifaniya daga gasar cin Kofin Duniya na shekara ta 2018 a zagaye na 16 wanda aka fafata a kasar Rasha kuma kasar Faransa ta samu nasara. Dan kasar Sifaniya din ya dawo gida ne saboda wasu dalilai kafin wasan da kasar ta samu nasarar cin 2-0 a Malta, lamarin da ya sanya aka maye gurbinsa da Moreno na wucin gadi haka kuma bayan wata uku ne Enrique ya sanar da matakinsa na ajiye aiki.

Mourinho Na Fatan A Sayo Masa Bale A Tottenham

Sabon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Jose Mourinho, yana fatan kungiyar ta sayo masa tsohon dan wasan ta, Gareth Bale, domin yana ganin zai taimaka masa wajen farfado da martabar kungiyar a halin yanzu.

Bayan da kungiyar ta maye gurbin Mauricio Pochettino da Mourinho a ranar Laraba, kungiyar tayi alkawarin zata bashi makudan kudade domin sayan sababbin 'yan wasan da zaiyi aiki dasu a kakar wasa mai zuwa.

Sai dai kamar yadda rahotanni daga kasar Ingila suka bayyana, Mourinho yana ganin kwarewar dan wasa Bale da kuma yanayin kasancewarsa tsohon dan wasan kungiyar zai sanya yaji yana bukatar sake komawa.

Bale dai ya kasance dan wasan da Tottenham baza ta manta dashi ba saboda irin kokarin da yayi a lokacin da yake buga mata wasa mafin kuma daga baya ya koma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a shekara ta 2013.

Mourinho dai zaiyi amfani da rashin jituwar da take tsakanin Bale da kociyan kungiyar, Zinadine Zidane wajen jan hankalin dan wasan ya amince ya koma kuma tuni suka shirya fara yiwa dan wasan Magana a watan Janairu mai zuwa.

A kwanakin baya Bale ya kusa komawa wata kungiya a kasar China da buga wasa kafin daga baya Real Madrida taki amincewa da cinikin kuma a halin yanzu yana da ragowar kwantiragin shekara biyu da rabi tare dasu.

Ramos Na Son Komawa Kasar Sin Da Buga Wasa

Wasu rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa dan wasan kuma kaftin din Real Madrid, Sergio Ramos, ya fara tunanin barin kungiyar inda yake tunanin komawa kasar China da buga wasa a kakar wasa mai zuwa. Tsohon dan wasan ya shafe shekara da shekaru a kungiyar inda ya buga wasanni 621 tun bayan komawarsa daga kungiyar Sebilla a shekara ta 2005 kuma ya lashe kofuna da dama a kungiyar da suka hada da laliga da kofin zakarun turai. Sai dai kusan shekara daya kenan aka fara rade radin cewa dan wasan na kasar Sipaniya yanason barin kungiyar domin komawa wata kungiya a kasar China wadda tayi masa alkawarin zata bashi albashi mai tsoka idan ya koma. Tuni dai aka bayyana cewa Ramos ya gama yanke hukuncin cewa zia koma kasar China da buga wasa a kakar wasa mai zuwa kuma shugaban kungiyar ta Real Madrid, Florentino Perez yasan da maganar tashin na Ramos. Kawo yanzu dais aura watanni 19 kwantiragin Ramos ya kare a kungiyar kuma bashi da niyyar sabunta yarjejeniyar cigaba da zaman kungiyar wanda hakan yasa kungiyar ta fara neman 'yan wasan bayan da zata maye gurbinsu. A kakar wasan data gabata ne Real Madrid ta sayi dan wasan baya daga kungiyar kwallon kafa ta FC Porto, Elder Militao kuma a yanzu haka yana bugawa kungiyar wasa sai dai kuma yanzu haka da kungiyar ta kara shiga kasuwa domin sayan dan dan wasan na baya.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China