Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon shugaban kasar Saliyo zai jagoranci tawagar AU don sanya ido a zaben kasar Namibiya
2019-11-27 13:35:19        cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta sanar a ranar Talata cewa, tsohon shugaban kasar Saliyo, Ernest Bai Koroma, ya tafi birnin Windhoek na kasar Namibiya a matsayin jagoran tawagar kungiyar AU mai sanya ido a zaben kasar Namibiyan wato (AUEOM), wanda ya za'a gudanar a yau Laraba.

Tsohon shugaban na Saliyo yana jagorantar tagawar mambobin kasashen AU 40 dake sanya ido a zaben kasar, tawagar da ta kunshi jakadu daga wakilan dindindin na kwamitin AU, da mambobin majalisar kasashen Afrika, da jami'an hukumomin zabe, da kungiyoyin fararen hula, da kwararrun masana harkokin zabe daga cibiyoyin nazari, kungiyar mai mambobin kasashen Afrika 55 ta bayyana hakan cikin wata sanarwa data fitar a jiya Talata.

Sanarwar tace, matakin tura tawagar AUEOM don sanya ido a zaben na kasar Namibiya ya kara tabbatar da aniyar kungiyar AU na goyon bayan tabbatar da samun sahihin zabe mai inganci kuma mai cike da zaman lafiya a dukkan kasashen mambobin kungiyar musamman ta hanyar sanya ido da bibiyar yadda ake shirya zabukan da yanayin da siyasar kasashen ke ciki.

Al'ummar kasar Namibiya zasu jefa kuri'unsu a yau Laraba domin zabar shugaban kasa da 'yan majalisun dokokin kasar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China