Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dandalin kirkire-kirkire a fannin tattalin arziki na shekarar 2019 na kokarin fidda sabuwar hanyar daidaita matsalar tattalin arzikin duniya
2019-11-25 14:55:50        cri

Kwanakin baya, an kira dandalin kirkire-kirkire a fannin tattalin arziki na shekarar 2019 a nan birnin Beijing, mai taken "Sabon tattalin arziki, sabuwar makoma", taron dake samun halartar jami'an gwamnati da tsoffin shugabannin kasashe daban-daban gami da 'yan kasuwa da masana fiye da 600, inda suka tattauna kan yadda za a warware matsalolin da duniya ke fuskanta a fannin tattalin arziki. Duk da cewa, ana fuskantar kalubaloli da sauye-sauye masu dimbin yawa, amma mahalarta taro na da imanin samun karuwar tattalin arzikin duniya nan gaba, sun nanata cewa, bude kofa da hadin kai muhimman matakai ne na warware matsalar da ake fuskanta.

Bankin Union na kasar Switzerland mai hadkwata a Zurich na kasar daya ne daga kamfanoni mafi girma a duniya dake sarrafa dukiyoyi, babban jami'i wato CEOn kamfani SergioP. Ermotti na goyon bayan shawarar "Ziri daya da hanya daya" da Sin ta gabatar, ya ce, kasarsa na bukatar wannan shawara sosai, kuma shawarar za ta amfanawa ayyukan manyan ababen more rayuwa da hada-hadar kudi da dai sauransu a nahiyar Turai. Ya ce:

"Mun tattauna kan ayyukan manyan ababen more rayuwa, kuma jarin da shawarar ta jawo ya samar da manyan sauye-sauye, don haka, shawarar na samun karbuwa sosai a kasarmu, saboda da ganin Turai na matukar bukatar muhimman ababen more rayuwar al'umma da dama."

Ban da wannan kuma, wani kwararre a fannin aikin yada labarai a Singapore dan asalin kasar Indiya, kuma manajan kamfanin FutureMap, Parag Khanna, wanda ya wallafa littafin da ya rubuta mai suna "Makomar duniya na cikin Asiya", ya nuna cewa, sama da rabin yawan mutanen duniya na Asiya, kuma nahiyar na ba da babbar gudunmawa ga tattalin arzikin duniya, shawarar kuma ta baiwa bunkasuwar tattalin arzikin duniya damammaki masu dimbin yawa. Ya ce kamata ya yi Sin da Indiya a matsayin kasashen dake da yawan mutane a duniya, su hada kansu a fannoni daban-daban don amfanawa jituwa da wadatar duniya gaba daya. Ya ce:

 "Wannan shawara ta baiwa kasashen da take shafa damammaki masu kyau a fannin samun bunkasuwa da raya manyan ababen more rayuwa da aikin zamanintar da al'umma. Indiya ba ta shiga wannan shawara ba, saboda wani dalili, amma wannan bai nuna cewa, Indiya ba ta amince da shawarar ba, a maimakon haka, Indiya na kan matsayi na biyu a cikin mambobin zuba jari ga bankin zuba jari na Asiya, kuma kasa mafi girma wajen ba da rancen kudi ga bankin, matakin da ya alamta cewa, hadin kan kasashen biyu na da muhimmanci sosai."

Yayin da duniya take fuskantar sabon kalubalen tattalin arziki, wasu mahalarta taron sun nuna cewa, ana bukatar habaka hadin kai da bude kofa. Bill Gates wanda ya kafa kamfanin Microsoft, kuma shugaban asusun Bill Gates da Melinda Gates ya ce, a fannin kwaikwayon hazikancin 'yan Adam na AI, ana iya samun bunkasuwa ta hanyar hadin kai, kuma rufe kofa zai haifar da koma baya. Ya ce:

"Ba za a iya dakatar da bunkasuwar fasahar AI ba ko kadan, wanda ke nacewa ga manufar bude kofa, zai zama sahun gaba a wanann fanni, a sa'i daya kuma, wanda ya rufe kofarsa, zai samu koma baya. Kuma wanda ba shi son bude kofa, za a yi biris da shi."

Dadin dadawa, dangantakar Sin da Amurka na jawo hankalin mahalarta taron sosai. Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka, kuma mai ba da taimako ga harkokin tsaron kasar kana shugaba mai daraja na dandalin, dakta Henry Kissinger ya nuna cewa, Amurka da Sin na sahun gaba a duniya ta fuskar tattalin arziki, saboda haka ana dora muhimmanci sosai kan dangantakar kasashen biyu. Yana sa ran dangantakar kasashen biyu za ta samu bunkasuwa mai kayu nan gaba, kuma ya mai da hankali sosai kan shawarwari tsakaninsu. Ya ce:

"A sabon halin da ake ciki, kamata ya yi kasashen biyu su ba da sabon bayani kan dangantakarsu, kuma su bi hanya iri daya wajen warware rikici tsakaninsu. Ina fatan a cimma nasara cikin shawarwarin da suka zama mafari ga shawarwarin siyasa da kasashen biyu za su gudanar. Ina fatan ganin an kara yin irin wannan shawarwari."

Shugaban bankin zuba jari ga manyan ababen more rayuwa na Asiya Jin Liqun ya yi kira ga Sin da Amurka da su kara hada kansu kan batutuwan dake shafar duniya, domin ba amfanawa kasashen biyu kadai zai yi ba, har ma da kawo babban alfanu ga duk duniya gaba daya.

Michael Bloomberg wanda ya kafa kamfanin Bloomberg L.P da asusun Bloomberg Philanthropies kana tsohon magajin birnin New York ne ya kafa wannan dandali a shekarar 2018, da zummar ingiza tattaunawa tsakanin manyan jami'an kasa da kasa kan canja salon bunkasuwar tattalin arzikin duniya da fidda hanyar warware manyan batutuwan duniya. An yi dandalin na farko daga ran 6 zuwa 7 ga watan Nuwamba na shekarar 2018 a Singapore. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China