Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'auni iri biyu na Amurka zai jawo ta shafawa kanta kashin kaji
2019-11-21 19:38:17        cri

Yau Alhamis, gidan rediyon kasar Sin ya gabatar da wani sharhi mai taken "Amurka tana amfani da ma'auni iri biyu, wanda hakan zai jawo ta shafawa kanta kashin kaji", inda aka yi nuni da cewa, dokar da majalisar dattijai ta Amurka ta zartas, kan hakkin dan Adam da demokuradiya na yankin Hong Kong na shekarar 2019, ba ta shafi demokuradiya ko hakkin dan Adam ba ko kadan, manufar dai ita ce nuna goyon baya ga masu tsattsauran ra'ayi, wadanda ke aikata laifuffuka a yankin Hong Kong, da nufin tayar da hargitsi a yankin, tare kuma da gurgunta ci gaban kasar Sin, amma yunkurinta ba zai cimma nasara ba, maimakon hakan zai bata sunan kasar Amurkan ne ita kanta.

Har kullum Amurka tana amfani da ma'auni iri biyu, a wurare daban daban, kuma duk wadannan sun nuna cewa, Amurka ta gamu da tabarbarewar siyasa, haka kuma ma'auni iri biyu da take amfani da shi, zai jawo ta shafawa kanta kashin kaji.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China