Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkaluman kididdigar tattalin arzikin Sin ya nuna alamu masu yakini
2019-11-21 10:52:24        cri

 

Jiya Laraba gidan rediyon kasar Sin ya fitar da wani sharhi mai taken "Alkaluman kididdigar tattalin arzikin Sin sun nuna alamu masu yakini".

Sharhin ya bayyana cewa, hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar da sakamakon kididdigar alkaluman tattalin arzikin kasar karo na 4 a wannan rana, inda aka nuna cewa, a cikin shekaru 5 da suka gaba tattalin arzikin kasar Sin na samun ci gaba mai inganci. Da farko, sana'ar hidima ta ci gaba cikin sauri, matakin da ya kara kyautatuwar tsarin tattalin arzikin kasar. Na biyu, muhallin gudanar da cinikayya na kara samun kyautatuwa, ana samun karuwar kasuwanni, ta yadda aka kara karfin ci gaban tattalin arzikin kasar mai inganci. Na uku, neman ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire ya kara tattara karfin neman ci gaban tattalin arzikin kasar mai inganci.

Sharhin ya kara da cewa, ko da yake ana fuskantar rashin tabbas a yayin da ake neman bunkasuwa, amma hali mai kyau da tattalin arzikin kasar Sin ya dade yana ciki, bai sauya ba, kasar Sin za ta mara baya matuka ga karuwar tattalin arzikin duniya. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China