Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana kokarin kyautata muhallin birnin Yan'an na lardin Shaanxi na kasar Sin
2019-11-23 14:24:22        cri


A cikin shirinmu na "Allah daya gari bamban", za mu yi muku bayani ne kan kokarin da mazauna birnin Yan'an na lardin Shaanxi na kasar Sin suke yi domin kyautata muhalli.

Birnin Yan'an yana kan tudun Loess, inda ake fama da matsalar karancin tsirrai da kuma tsananin zaizayar kasa, a cikin shekaru 20 da suka gabata, mazauna birnin Yan'an suna nacewa kan manufar dasa itatuwa a gonakin da ba su dace da shuka hatsi ba, wato sun daina shuka hatsi a kan gonakin, inda ake fama da matsalar tsananin zaizayar kasa bisa matakai daban daban, domin dasa itatuwa a kansu, ta yadda za a maido da gandun daji a wurin tare kuma da kara kyautata muhallin halittu masu rai da marasa rai.

Birnin Yan'an ya yi suna ne bisa matsayinsa na tsohon wurin juyin juya hali domin kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, a halin da ake ciki yanzu, mazauna birnin suna gudanar da wani sabon juyin juya hali na kiyaye muhalli, bisa manufar raya kasa da babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya gabatar wato ita ce "Ruwa mai tsabta da duwatsu masu launin kore, dukkansu dukiyoyi ne", har sun sauya launin wurin daga rawaye zuwa kore.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China