Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hamshakin dan kasuwan kasar Sin na kokarin tallafawa matasa masu kamfanoni na Afirka
2019-11-18 14:28:47        cri

A ranar 16 ga watan da muke ciki, aka kammala gasar masu kamfanoni na Afirka da asusun hamshakin dan kasuwan kasar Sin Ma Yun ya gudanar, a Accara na kasar Ghana. Inda aka ba masu kamfanoni 10 wadanda suka ci nasarar gasar kyautar kudi da yawansa ya kai dalar Amurka miliyan daya.

A watan Fabrairun bana, aka kaddamar da asusun Ma Yun na tallafawa masu kamfanoni na Afirka, tare da burin samar da dala miliyan 10 a cikin shekaru 10 masu zuwa, ga 'yan kasuwa matasa na kasashen Afirka. Matasan 10 da suka shiga mataki na karshe na gasar masu kamfanoni na Afirka na wannan karo sun fito ne daga kasashen Masar, Najeriya, Laberiya, Ruwanda, da kuma Kodibwa, yayin da sana'o'insu suka shafi aikin gona, da likitanci, da kwaliya, da samar da takalma, da na'urorin da ake bukata wajen gudanar da ayyukan kimiyya da fasaha, da dai makamantansu. A wajen taron masu kamfanoni na Afirka da ya gudana a gefen gasar ta wannan karo, mista Ma Yun, ya ce ana samun isashen albarkatu da damammaki a nahiyar Afirka, sai dai ana bukatar mutane wadanda za su kirkiro sabbin fasahohi gami da gwajinsu, tare da canza yanayin nahiyar Afirka gaba daya. Ya ce, "Masu kamfanonin da suka halarci wannan gasa za su taimakawa nahiyar Afirka raya harkokin kasuwanci, za su kuma wayar da kan karin mutane domin su canza zaman rayuwarsu, gami da neman cika burinsu. Muna fatan ganin sun ci nasara, ta yadda za a samarwa nahiyar Afirka karin damammaki. "

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, shi ma ya halarci taron da ya gudana a Accara, inda ya godewa mista Ma Yun, kan yadda ya kaddamar da asusun tallafawa masu kamfanonin Afirka. A wurin da aka gudanar da zagayen karshe na gasar masu kamfanonin Afirka, shugaban ya ce,"Ya kamata mu yi kokari tare don raya nahiyar Afirka, da baiwa zuriyoyi masu zuwa abubuwan da za su yi gado. Kar mu yi watsi da wannan dama. Ta hanyar taimakawa masu kamfanoni, da kyautata muhallin kasuwanci, za a samu damar raya tattalin arziki cikin sauri."

Masu kamfanoni 10 da suka shiga zagayen karshe na gasar masu kamfanonin Afirka, su ne gwanayen da aka fid da daga cikin mutane fiye da dubu 10 da suka shiga gasar, wadanda suka zo daga kasashe fiye da 50 na nahiyar Afirka. A wajen zagayen karshe na gasar, sun nuna ma mista Ma Yun, da sauran alkalan gasar, ayyukan da suke yi. A karshe, mai kamfani na kasar Najeriya, Temie Giwa-Tubosun, ta larshe gasar bisa kamfanin da ta bude mai sunan "Bankin rayuka". Wannan kamfani na yin amfani da wasu bayanai da fasahohi na zamani wajen taimakawa likitoci ganin magunguna da na'urorin da suke bukata a kokarin jinyar mutane. Ta wannan hanya, an samu damar kubutar da mutane fiye da 5300 a kasar Najeriya. A wajen bikin ba da kyauta, Malama Temie ta ce, "Ina farin ciki matuka. Saboda na yi imani da wajibcin karfafa wa matan Afirka gwiwa, domin su rike wani babban buri, da kokarin neman daidaita matsalolin dake addabar al'ummunmu. Hakika matan Afirka sun riga sun fara yin haka."

An ce, masu daukar nauyin tsara gasar masu kamfanonin nahiyar Afirka sun nemi tsara wani shirin telabijin na musamman mai taken " Jaruman kasuwanci na Afirka", inda za a dinga nuna kwararrun 'yan kasuwan Afirka da harkokinsu, don ci gaba da karfafa wa matasa masu kamfanoni na kasashen Afirka gwiwa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China