Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ra'ayoyin masanan Brazil da Indiya kan tsarin BRICS
2019-11-15 14:53:11        cri





A ranar 13 ga wata ne, aka rufe taron dandalin tattaunawar masana'antu da kasuwanci na kasashen BRICS a birnin Brasilia, fadar mulkin kasar Brazil, kuma shugaban kasar Xi Jinping ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi.

Masanan kasashen Brazil da Indiya sun bayyana cewa, a jawabin da ya gabatar, shugaba Xi Jinping ya jaddada niyyar kasar Sin ta kara bude kofarta ga kasashen waje, kuma a kokarin da kasar Sin ke yi na kara bude kasuwarta.

A jawabin da ya gabatar, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, ci gaban kasar Sin dama ce ga kasashen duniya. Kasar Sin ba ta sauya niyyarta ta kara bude kofarta ga kasashen waje ba, kuma za ta ci gaba da bude kasuwarta, da kuma kara shigowa da kayayyaki daga kasa da kasa, za ta kuma dinga kyautata yanayin gudanar da harkokin kasuwanci a kasar. A game da wannan, shehun malami a jami'ar Rio de Janeiro MaurĂ­cio Santoro, ya bayyana cewa, Sin ta kasance kasuwa mafi girma a duniya, wadda ke samar da damammaki ga kasashen da suka hada da Brazil, kuma manufar kasar Sin ta kara bude kofarta ma, ta kiyaye tsarin ciniki cikin 'yanci na duniya. Ya ce, "A yayin da muke ta fama da matsalar kariyar ciniki, kasar Sin ta ba da babbar gudummawa ta fannin kiyaye 'yancin ciniki a duniya. A sa'i daya kuma, Brazil ma tana tattauna kara bude kasuwarta, ma iya cewa burinmu daya ne. A yayin da muke neman kara bude kasuwanninmu, Brazil ta kasance wata muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa ga kasar Sin."

Hadin gwiwar tattalin arziki yana daga cikin fannonin da aka fi cimma nasarori, kuma mafi muhimmanci a hadin gwiwar kasashen BRICS. A jawabin da ya gabatar, shugaba Xi Jinping ya kuma yi nuni da cewa, ya kamata 'yan kasuwa da ma masu masana'antu, su rike damammakin da suke fuskanta, kuma su yi kokarin shiga hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen. A game da wannan, MaurĂ­cio Santoro ya ce, yanzu haka masu masana'antun ba su samu cikakkiyar masaniya a kan muhimmancin tsarin BRICS ba, ya ce, "Kamata ya yi a wayar da kan masu masana'antun kasashen BRICS, kan ma'anar tsarin BRICS, sabo da ganin yadda da yawa daga cikinsu, ba su da cikakkiyar fahimtar muhimmancin tsarin. 'Yan kasuwa da masu masana'antu na taka muhimmiyar rawa a hadin gwiwar kasashen BRICS."

Kasancewarta kasa mai karfin tattalin arziki da ma yawan al'umma daga cikin kasashen kungiyar BRICS, kasar Indiya na taka muhimmiyar rawa ga tsarin hadin gwiwar BRICS. Prof. B. R. Deepak, shehun malami ne a cibiyar nazarin harkokin kasar Sin, da na kudu maso gabashin Asiya a jami'ar Jawaharlal Nehru ta kasar Indiya, yana kuma ganin cewa, a yayin da ake ta kara fuskantar ra'ayin kashin kai a duniya, tsarin BRICS yana da muhimmiyar ma'ana. Ya ce, "Idan mun yi la'akari da yanayin tattalin arzikin duniya, da ma rawar da kasashen BRICS ke takawa, ciki har da yawan tattalin arzikin kasashen da al'ummunsu, da kasuwanninsu, da ma taimakon da suke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin duniya, musamman a lokacin da ake ta kara fuskantar matsalar kariyar ciniki, tsarin na da muhimmiyar ma'ana, idan mun yi la'akari da shi ta wadannan fannoni."

Prof. B. R. Deepak ya kara da cewa, nan da shekaru 10 masu zuwa, tsarin hadin gwiwar kasashen BRICS, zai kara fuskantar damammaki da kalubale. Sin abin koyi ce ga kasa da kasa ta fannin kirkire-kirkiren fasahohi, kuma hadin gwiwar kasa da kasa zai taimakawa kasashen BRICS, wajen kasancewa muhimmin karfin da ke sa kaimin ci gaba da kirkire-kirkire a duniya. Ya ce, "Kasancewar Sin babbar kasa, musamman kasar da ta fi karfin tattalin arziki cikin kasashen BRICS, ta samu gaggarumin ci gaba ta fannonin fasahohin zamani, da suka hada da AI da 5G da sauransu. A gani na, ya kamata kasashen BRICS su kara hadin kansu a fannin fasahohin, wadanda za su haifar da babban tasiri ga tattalin arziki, da ciniki, da cudanyar al'umma, da ma rayuwar daidaikun mutane." (Lubabatu Lei)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China