Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a cimma hasashen da aka yi kan karuwar tattalin arzikin Sin
2019-11-14 20:45:53        cri

Yau Alhamis 14 ga wata hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar da wasu alkalumu dake nuna cewa, duk da tafiyar hawainiya da tattalin arzikin duniya ke yi, tattalin arzikin kasar yana gudana cikin lumana a cikin watanni goma na farko na bana, haka kuma duk da yadda tattalin arzikin duniya ke fuskantar yanayin rashin tabbaci, amma tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba yadda ya kamata.

An samu wadannan nasarori ne, saboda kasar Sin tana aiwatar da manufofin da suka dace, kamfanonin kasar su ma suna mai da hankali kan kirkire-kirkire, kana tun a farkon bana, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar rage harajin da take bugawa kamfanonin kasar, da ma rage harajin da ya kai kudin Sin yuan biliyan 2000, a sa'i daya kuma, kasar ta fitar da wasu matakai domin saukaka cinikayya, tare kuma da kyautata muhallin kasuwanci a kasar.

A yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar daga waje karo na 2 da aka kammala ba da dadewa ba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da matakai biyar domin kara bude kofa ga waje, tare kuma da samar da muhallin kasuwanci mai inganci ga 'yan kasuwa baki domin zuba jari a kasar ta Sin.

A bisa wannan yanayin, kasuwar cikin gidan kasar Sin tana kara habaka, ana sa ran cewa, kasar Sin za ta cimma hasashen da aka yi kan karuwar tattalin arzikinta.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China