Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban CMG: Abun da kafofin watsa labaran kasashen yamma suka fada kan HK ba gaskiya ba ne
2019-11-14 20:04:23        cri

A ranar 12 ga wata, jaridar "Folha de Sao Paulo" ta wallafa wani sharhi da wakilinta Nelson de Sa ya rubuta mai taken "Yadda kafofin watsa labarai ke ba da rahoto kan Hong Kong ba gaskiya ba ne, shugaban CMG ya ce, kafofin watsa labarai na yammacin duniya ba su fadi gaskiya ba".

Cikin sharhin, ya ce, shugaban babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong ya ce, labaran da kafofin watsa labarai na yammacin duniya suka rubuta game da yankin Hong Kong na kasar Sin ba su nuna gaskiyar halin da yankin ke ciki ba.

A cikin bayanin, an ce, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, ya kasance kafar watsa labaru mafi girma a duk duniya, shugaban rukunin CMG Shen Haixiong ya bayyana a ran 11 ga watan a birnin São Paulo na kasar Brazil, cewa, ya kamata a ayyana ayyukan da ake yi a yankin Hong Kong a matsayin ayyukan nuna ta'addanci, ba wai matakan yin zanga-zanga kawai ba.

Mr. Shen Haixiong ya kuma zargi wasu kafofin watsa labaru na yammacin duniya kan rahotannin da suka bayar game da batun Hong Kong, cewar rahotannin da suka bayar, ba su bayyana gaskiyar abubuwa da suke faruwa a yankin kasar Sin ba. "Wasu kafofin watsa labarun yammacin duniya, musamman kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun zabi wasu abubuwan da suke so, sannan suka kaucewa fadin gaskiya." Mr. Shen ya kara da cewa, "Wallahi, shugaban kasarsu Donald Trump ma bai amince da rahotannin da wasu kafofin watsa labaru na Amurka suka bayar ba."

Mr. Shen ya kuma nuna cewa, "Abin da nake son bayyanawa shi ne, ina fatan kafofin watsa labarai, za su rika watsa labarun daidai da abubuwan da suke faruwa a yankin Hong Kong, wasu abubuwan da ma boren ke aikatawa a yankin, tamkar ayyukan ta'addanci ne." Yana mai cewa, a karshen makon da ya gabata, wani mai zanga-zanga ya ji rauni, amma a bangare guda shi ne, an zubawa wani mutum man fetur a jikinsa, aka kuma cinna masa wuta, ba don komai ba, saboda ya yi cacar baki kawai da masu zanga-zanga

Mr. Shen, a matsayinsa na tsohon dan jarida, ya yi shekaru da yawa yana aiki a kamfanin dillancin labaru na Xinhua. A ganinsa, wasu kafofin watsa labaru na arewacin nahiyar Amurka ba su kware a ayyukan da suke yi ka ba, ko kuma suna take dokokin aikin, sabo da da farko dai, dole ne a girmama gaskiya. 

Game da batun yadda gwamnatin kasar Sin ke sa ido kan kafofin watsa labaru, Shen Haixiong ya ce, "Sinawa ba su da korafi kan yadda ake sanya ido a shafukan yanar gizo ta Internet, maimakon haka suna mamakin yadda ake watsa karairayi game da kasar Sin kan shafukan Internet da yawa."

Wannan babban jami'i ya zo kasar Brazil a wannan karo, domin yiwa shugaban kasar Xi Jinping rakiya, wanda ke halartar taron ganawa tsakanin shugabannin kasashen BRICS a Brasilia da aka fara a ranar 13 ga wata, gami da sake ganawa da shugaba na kasar Brazil, Jair Bolsonaro, wanda ya ziyarci kasar Sin a watan da ya gabata.

Lokacin da ya isa birnin Sao Paulo, Mista Shen ya sa hannu kan yarjejeniyar hadin kai da aka kulla tsakanin babban gidan rediyo da telabijin kasar Sin CMG, da Grupo Bandeirantes de Comunicação na kasar Brazil, kan musayar bayanai, da hadin gwiwar tsare shirye-shirye.

A cewar jami'in, hadin gwiwar da ake yi yanzu ta tsaya kan cudanya ce a fannin watsa labarai kawai, maimakon neman kulla hulda ta kasuwanci. "Yanzu ba mu da niyyar zuba jari a kamfanonin watsa labari na kasar Brazil." In ji jami'in.

Makonni uku da suka gabata, Mr. Shen Haixiong ya tarbi Osmar Terra, ministan harkokin al'umma na kasar ta Brazil a birnin Beijing, wanda ya ba da shawarar samar da wata kafar talabijin ta Brazil a kasar Sin, don watsa shirye-shiryen talabijin da fina-finai, da kuma samar da wata kafar kasar Sin irin wannan a kasar ta Brazil."

A lokacin da aka tambaye shi ko yana so a kaddamar da shirye-shiryen kafar CGTN a kasar Brazil, ya amsa da cewa, "Wannan zabi ne mai kyau, kuma mataki ne da za a iya dauka", sai dai bai yi karin haske ba.

Mr. Shen ya kara da cewa, yarjejeniyar da CMG ya cimma tare da Grupo Bandeirantes de Comunicação da ma shirye-shiryen da za a fara watsawa bisa yarjejeniyar sun alamta sabon mafari na hadin gwiwar sassan biyu. Yana mai cewa, "Za mu kara ingiza hadin gwiwarmu daga dukannin fannoni."

Dangane da ziyarar da Jair Bolsonaro ya kai kasar Sin makonni 3 da suka wuce da kuma kudurin Sin da Brazil na zurfafa hadin gwiwar da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, ya jaddada cewa, lokaci ya yi da CMG da kamfanin Grupo Bandeirantes de Comunicação za su hada kansu.

Wannan babban jami'i ya nuna cewa, manufar CMG ita ce kafa wata kafar yada labaru ta kasa da kasa, wadda ke mai da hankali kan yin amfani da fasahar zamani cikin bidiyo. Ya ambato batutuwan fasahar 8K, 5G da AI da watsa labaru a shafukan sada zumunta.

Yayin da bangarorin 2 suka daddale yarjejeniyar, shugaban kamfanin Grupo Bandeirantes de Comunicação ya ce, hadin gwiwar ta burge shi sosai, musamman ma shirin talabijin na "Labarun da Xi Jinping yake sha'awa", wanda a cewarsa, ya ilmantar da mutane ta fuskar ilimin falsafa da dimokuradiyya.

João Doria, shugaban jihar São Paulo da ya halarci bikin daddale yarjejeniyar, ya nuna cewa, ya karanta littafin Xi Jinping, zai kuma ziyarci kasar Sin a shekara mai zuwa tare da shugabantar kungiyoyi guda 2, wato na shugabannin jihohin kudancin kasar da na kudu maso gabashin kasar da kuma na 'yan kasuwan São Paulo. Doria ya kuma yi hasashen cewa, kasar Sin za ta zuba jari na farko a São Paulo a fannin jirgin karkashin kasa, lamarin da zai kara azama kan mayar da kadarorin gwamnatin hannun 'yan kasuwa.

Game da shirin "Labarun da shugaba Xi Jinping yake sha'awa" na harshen Girka, tsohon ministan kula da ci gaban masana'antu da cinikayya jakada Sérgio, ya ce irin wannan hadin gwiwa ta dace da ra'ayin 'yan kasuwar Brazil, burinsa shi ne "Kara fahimtar juna a fannin al'adu a tsakanin bangarorin biyu".

"Karuwar matsayin kasar Sin a dandalin duniya, shi ne 'hakikanin halin da ake ciki' a yanzu". Ba kawai kasar Sin ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ta Brazil da wasu kasashen Latin Amurka da dama ba, har ma za a bullo da wasu sabbin fannonin da za a samu ci gaba a kai, kamar zuba jari." Jakadan ya kara da cewa, "A cikin 'yan shekaru kadan kasar Sin ta kara zuba jarin da ya kai dala biliyan 70 a kasar Brazil, kuma adadin na ci gaba da karuwa a yanzu haka." (Masu Fassarawa: Maryam, Sanusi, Bello, Lubabatu, Tasallah, Bilkisu daga CRI Hausa)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China