Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Qishan: Sin na dora muhimmanci ga wanzar da zaman lafiya da martaba dokokin kasa da kasa
2019-11-14 10:09:12        cri
Mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan, ya ce Sin na dora muhimmancin gaske ga sha'anin wanzar da zaman lafiya, da kuma martaba dokokin kasa da kasa, baya ga gudummawar da take bayarwa wajen ciyar da duniya gaba.

Wang Qishan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin bikin bude taron tattaunawa game da zaman lafiya da ke gudana yanzu haka a birnin Paris na kasar Faransa. Ya ce "Mun daura damarar aiki tare da dukkanin kasashe domin samar da al'ummar duniya mai makoma guda, da kulla huldar kawance ta kasa da kasa bisa tushen martaba juna, da daidaito, da adalci da hadin gwiwa na cimma moriyar juna".

Wang Qishan ya ce ta hanyar daukar sahihan matakai, kamar fadada aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", da gudanar da baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, da rage hajoji da sassan da a baya Sin ta hana zuba jarin waje a cikin su, da kuma kyautata yanayin gudanar da kasuwanci, Sin na samar da karin damammakin ci gaba ga sauran sassan duniya.

Ya ce "Muna da karfin gwiwar kaiwa ga gina duniya maras fama da yake-yake da talauci, duniya mai cikakken tsaro da wadata ga kowa".

Taron dai na tattauna batutuwan da suka jibanci zaman lafiya, ya samu halartar shugabannin kasashen duniya, da wakilan kasashe sama da 80, baya ga manyan jami'ai, da jagororin hukumomin kasa da kasa da na yankuna da dama da suka halarta. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China