Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sassa daban daban na kasar Girka sun zura ido kan ziyarar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi a kasarsu
2019-11-13 14:37:32        cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya gudanar da ziyarar aiki a kasar Girka tsakanin ranekun 10 zuwa 12 ga wata. Sassa daban daban na Girka sun zura ido kan ziyarar da shugaba Xi Jinping ya yi a kasarsu, sun kuma yaba wa sakamakon hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2.

George N. Tzogopoulos, wani masanin ilmin al'amuran kasa da kasa na kasar Girka, kuma darektan kula da shirin Turai da kasar Sin, a cibiyar duniya kan nazarin Turai, ya bayyana a birnin Athens cewa, ziyarar shugaba Xi Jinping na kasar Sin a wannan karo tana da muhimmiyar ma'ana, ta kuma alamta cewa, kasar Sin tana maida hankali kan raya hulda a tsakaninta da kasar Girka, kuma tabbas ziyarar za ta kara sabon kuzari kan hadin gwiwar a-zo-a-gani a tsakanin kasashen 2. "Kasar Sin tana himmantuwa wajen daga huldar da ke tsakaninta da kasar Girka zuwa sabon matsayi. Wannan ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kawo wa kasarmu ziyarar aiki bayan shekaru 11. Na yi imani da cewa, ziyararsa za ta kara azama kan bunkasuwar dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen 2, bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni." Gwamnatin kasar Girka na sa muhimmanci kan bunkasa hulda a tsakaninta da Sin. Nan da watanni da dama masu zuwa, kasashen 2, za su kara tattaunawa kan hadin gwiwarsu, tare da daukar karin matakai."

Mista Tzogopoulos ya kara da cewa, shugabannin kasashen 2 sun ganewa idonsu, musayar takardun hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2, wadanda suka shafi zuba jari, da tashar jiragen ruwa, hada-hadar kudi, makamashi, ilmi da dai sauransu, hakan ya kuma kasance a matsayin muhimmin sakamako na ziyarar shugaba Xi Jinping. Wannan masani yana ganin cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin Girka da Sin tana amfani ga kyautatuwar dangantakar da ke tsakaninsu, da ma ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Turai.

Mataimakin ministan ilmi na kasar Girka Vassilis Digalakis, ya bayyana cewa, kasashen Sin da Girka, kasashe ne masu dogon tarihi ta fuskar al'adu a duniya. Ya ce mu'amala a tsakaninsu, da koyi da juna, suna da muhimmanci sosai. A cewar sa, kasashen suna fuskantar kyakkyawar makoma wajen yin hadin gwiwa a fannin ilmi. Ziyarar shugaba Xi Jinping za ta kara azama kan hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 a wannan fanni. "Muna fatan kara yin hadin kai a tsakanin jami'o'in kasashen 2, da ma kasashen 2, muna hada kai a wannan fanni. Nan gaba muna fatan za a gudanar da karin shirye-shiryen hadin gwiwa tsakanin jami'o'in kasashen 2. Alal misali, daliban kasar Sin za su samu damar koyon tarihin Girka da al'adun kasar, yayin da dalibanmu za su samu damar koyon tarihin kasar Sin, al'adunta da harshenta."

Haka zalika, ziyarar da shugaba Xi Jinping ya yi a kasar ta Girka ta jawo hankali sosai a tsakanin mazauna wurin. Tina Demetriou, wadda ke zaune a Athens ta gaya mana cewa, kasashen Girka da Sin sun shirya kara hada kai a fannonin zuba jari, tashar jiragen ruwa, hada-hadar kudi da makamashi, wadanda al'ummar kasar ke zura ido a kai. "Kasar Sin tana da karfin tattalin arziki, kasarmu na bukatar hada kai da ita. Muna bukatar masu yawon shakatawa daga kasar Sin. Muna maraba da ziyarar su a kasarmu. Na yi imani da cewa, idan an aiwatar da wadannan yarjejeniyoyin hadin gwiwa, al'ummun Girka masu yawa za su samu aikin yi. Bunkasuwar tattalin arziki zai taimaka wa karin mutane su samu aikin yi."

Wani mazaunin birnin Athens mai suna Thanos Papadakis ya ce, ya san cewa, kasashen Girka da Sin za su inganta hadin gwiwa ta fuskar yawon shakatawa bisa bayanai da aka gabatar. Yana alla-alla wajen ganin hadin gwiwar ya amfani abokansa da iyalinsa. "Kasar Sin wata kyakkyawar kasa ce. Tun can da ina fatan zuwa kasar Sin. Yanzu mutanen Sin da yawa suna zuwa kasarmu ziyara. Abokaina da iyalina, su ma suna fatan ziyartar kasar Sin. Dukkan kasashenmu na da dogon tarihi." (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China