Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yang ya ziyarci cibiyar baje kolin kirkire-kirkire ta kamfanin Huawei dake Masar
2019-11-13 09:59:14        cri
A ranar Litinin ne shugaban kwamitin kasa na majalissar bada shawara kan harkokin siyasar ta kasar Sin Wang Yang, ya ziyarci cibiyar baje kolin kayayyakin kirkire-kirkire ta kamfanin Huawei reshen yankin arewacin Afirka dake birnin Alkahira na kasar Masar, inda ya ganewa idanunsa na'urorin zamani, da sabbin fasahohin da kamfanin ya samar, musamman wadanda suka shafi kula da iyali, da na zamanantar da ayyukan kula da birane. Kaza lika ya kalli wasu faye-fayen bidiyo da aka sarrafa ta fasahar 5G, da 5G+VR.

Bayan nazartar ci gaban da kamfanin ke samarwa ta fannin raya fasahohin zamani, Mr Wang ya yi kira ga mahukuntansa da su zage damtse wajen fadada dabarun bunkasa kamfanin, ta yadda tasirinsa zai yadu zuwa dukkanin sassan duniya, ya kuma amfani kasashen da yake gudanar da harkokinsa.

Daga nan sai ya jinjinawa kamfanin na Huawei, bisa jajircewarsa wajen amfani da dabarun kirkire-kirkire wajen raya masana'antu, da shiga a dama da shi a fannin hadin gwiwar kasa da kasa domin samar da ci gaba. Ya ce baya ga ci gaban da Huawei ya samu, ya kuma habaka cin moriyar juna tsakaninsa da kasashen da yake gudanar da harkokinsa.

Yayin wannan ziyara, mahukuntan kamfanin sun yiwa Mr. Wang karin haske game da shirin kamfanin na aiwatar da manufofin sa, da zuba jari, da gudanar da bincike, da ci gaba, da ma kudurorin da kamfanin ya sanya gaba. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China