Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan kayayyakin da aka sayar a ranar gwagware ya nuna yadda tattalin arzikin kasar Sin ke kara karfi
2019-11-12 19:58:18        cri
Ba da jimawa ba da kammala bikin baje kolin kayayyakin da aka shigo da su kasar Sin karo na biyu, sai kuma nan da nan aka shiga ranar gwagware ta ranar 11 ga watan Nuwamba a kasar Sin, yawan kayayyakin da aka sayar a bukukuwan biyu sun nuna karfin kasuwar kasar na sayen kayayyaki. A yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke fuskantar rashin tabbas a waje, kyakkyawar alama da kasuwar kasar ta nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin na da makoma mai kyau, kuma yana cike da karfin tinkarar duk wani hadari da ka iya kunno kai.

 

Shagon sayar da kayayyaki ta Intanet na rukunin kamfanin Alibaba wato TMall ya kara shigar da wasu sabbin tambarun kaya daga kasashen ketare, wadanda karuwar ta ninka sau uku bisa na makamancin lokacin bara, galibi daga Amurka, Burtaniya, Japan da kuma sauran kasashen yammacin duniya. Yadda suke kokarin neman shiga kasuwar kasar Sin, ya nuna cewa, maganar " raba gari ta fannin tattalin arziki" a tsakaninsu da kasar ta Sin, abu ne maras tushe, kuma ba zai faru ba.

 

 

Harkokin sayayya na taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arziki. Don haka, babbar kasuwar cikin gida ita ce ginshikin tattalin arzikin kasar Sin wajen fuskantar kalubale daga ketare da ci gaba da yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga ketare. (Ma'aikaciyar Sashen Hausa: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China