Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron hadin kan makamashi na duniya na shekarar 2019
2019-11-07 15:12:14        cri


Jiya Laraba, an bude taron hadin kan makamashi na duniya na shekarar 2019 kana taron makamashin wutar lantarki tsakanin Sin da Afrika a cibiyar taro ta birnin Beijing. Taron dai da ya shafe kwanaki biyu ana yinsa ya samu halartar wakilai fiye da 1000 daga kasashe 79, inda suka tattauna yadda kasashen duniya da Afrika za su hada kai ta fuskar makamashi bisa taken "Hadin kan kasa da kasa kan makamashi-hanyar samun bunkasuwa mai dorewa maras gurbata muhalli" da "Hadin kan kasashen Afrika kan makamashi-sabon karfin raya nahiyar Afrika", matakin da ya samar da sabon tafarkin zamanintar da makamashi da samun bunkasuwa mai dorewa.

Kasar Sin ta shawarci kasashen duniya, da su hada kai a fannin makamashi a gun taron koli na samun bunkasuwa na MDD da ya gudana a watan Satumba na shekarar 2015. A cikin shekaru 4 da suka gabata, wannan shawara ta samu karbuwa a duniya tare da samun ci gaba mai armashi. Ya zuwa yanzu, an shigar da tsarin hadin kan kasa da kasa kan makamashi cikin wasu tsare-tsaren ayyuka ciki hadda shawarar "Ziri daya da hanya daya", ajandar samun bunkasuwa mai dorewa na shekarar 2030 ta MDD, aikin ingiza aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, aikin gaggauta daidaita matsalar muhallin duniya, da na warware matsalar karancin wutar lantarki da dai sauransu. Matakin da ya kai ga kammala wasu manyan ayyukan share fage ta fuskokin tsari da fasaha da na'urori da ma'auni dangane da aikin bullo da tsarin hadin kan kasa da kasa kan makamashi. Mataimakin magatakardan MDD Liu Zhenmin ya bayyana cewa,

"Wannan tsari ya taimakawa kasashe masu tasowa wajen yin amfani da makamashi mai tsafta, da gaggauta zamanintar da makamashi, da ingiza cimma muradun samun bunkasuwa mai dorewa, da tallafawa kasashen Afrika wajen samun tsaftaccen makamashi mai inganci kuma maras tsada, da kuma daidaita hanyar samun makamashi mai sauki ta yadda za a taimakawa kokarin da ake na kafa al'umma mai dauwamammen ci gaba da jituwa cikin lumana. Taron na wannan karo, ya kasance wani muhimmin dandalin neman hadin kai da more ilmi da kuma tattara fasaha da jari."

Taron na wannan karo ya mai da hankali sosai wajen yayata shawarar da kasar Sin ta gabatar game da bullo da tsarin hadin kan kasa da kasa kan makamashi, wanda ya kunshi sassa daban-daban, ciki hadda gabatar da jawabai da yin tattaunawa, da gabatar da sakamakon ci gaban da aka samu, da kulla yarjeniyoyi, da baje kolin na'urori na zamani da Sin take da su, da zummar karawa bangarori daban-daban kwarin gwiwar hada kai wajen raya manyan ayyukan samar da wutar lantarki a Afrika da ma duniya baki daya, da ingiza raya makamashi mai tsabta da hadin kan kasa da kasa ta fuskar wutar lantarki, ta yadda za a sa kaimi ga sha'anin hadin kan kasa da kasa dangane da makamashi a duniya. Shugaban kungiyar raya tsarin hadin kan kasa da kasa kan makamashi kana shugaban kungiyar kamfanonin wutar lantarki ta kasar Sin Liu Zhenya ya bayyana cewa,

"Tsarin hadin kan kasa da kasa kan makamashi wani muhimmin dandali ne wajen raya makamashi mai tsafta da raba shi da ma amfani da shi a duk fadin duniya, ayyukan da aka yi shi ne tsarin samar da wutar lantarki na zamani da tsarin wutar lantarki mai karfi da tsabtaccen makamashi. A cikin shekaru 10 da wani abu da suka gabata, Sin ta himmatu wajen raya fasahar tsarin samar da wutar lantarki mai karfi, inda ta kafa ayyuka 24 a wannan fanni, yayin da ake kokarin kafa wasu 8 a halin yauzu, wannan tsari ya zama irinsa mafi girma a duniya, dake iya tafiyar da ayyukansa lami lafiya, matakin da ya ingiza bunkasuwar makamashi mai tsafta a kasar Sin."

Ban da wannan kuma, taron ya dora muhimmanci kan hadin kan Sin da Afrika kan makamashin wutar lantarki da kafa tsarin hadin kan kasashen Afrika kan makamashi, a kokarin aiwatar da wannan shawarar da taron ya gabatar a nahiyar, matakin da zai kasance jagora ga manyan ayyuka guda 8 dangane da hadin kan Sin da Afrika. Wakilai fiye da 200 daga kasashen Afrika kimanin 30 ne, suka halarci taron, mataimakin shugaban hukumar makamashi ta kasar Sin Liu Baohua ya nuna cewa, Sin da Afrika sahihan abokai ne dake da dankon zumunci, kana suna da makoma mai haske a fannin hadin kansu da cin moriyar tare, taron ya samar da wani muhimmin dandali ga bangarorin biyu wajen ingiza da zurfafa hadin kai ta fuskar makamashin wutar lantarki da ma'adinai da dai sauransu. Ya ce:

"Ina so in gabatar da shawarwari guda 3, na farko, ya kamata hukumomin gwamnatoci da kungiyoyin kasa da kasa da hukumomin nazari da kuma kamfanonin Sin da Afrika su kara tuntubar juna ta fuskar manufofi, kara cudanya da amincewa da juna da kuma zurfafa hadin kansu; na biyu kuma, bangarorin Sin da Afirka su kara yin cudanya da hadin kai wajen kirkire-kirkiren fasahohin makamashi don taimakawa juna da cin moriya tare; na uku kuwa, a sa kaimi ga hada na'urorin bangarori biyu waje guda.".

Bayanai na cewa, taron zai gabatar da muhimman rahotanni 3 dangane da hadin kan makamashi tsakanin Sin da Afrika, domin taimaka wa kasashen Afrika wajen raya makamashi mai tsabta da raba shi zuwa ketare, da ma hadin kan kasashen Afrika a fannin wutar lantarki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China