Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta dauki matakan kara tabbatar da kyautatuwar rayuwar al'ummun birane da kauyuka
2019-11-06 20:12:43        cri
Wani kundin bayani mai kunshe da kudurin da kwamitin kolin JKS ya amincewa, ya ce Sin za ta dauki matakan hade sassan tsare tsare, na tabbatar da kyautatuwar rayuwar al'ummun yankunan birane da na karkarar kasar. Kundin ya bayyana daukar wannan mataki a matsayin hanyar cika muradun al'ummar Sinawa, na samun rayuwa mai nagarta.

Kaza lika kundin ya ce an amince da wadannan matakai na kyautata tsare tsare ne, domin tabbatar da nasarar jagorancin kasar, bisa salon gurguzu mai halayyar musamman na Sin, da kuma bunkasa zamanintar da salon mulkin kasar yayin taro na 4, na kwamitin kolin JKS karo na 19, wanda ya gudana a ranar 31 ga watan Oktoba. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China