Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Al'ummomin duniya sun yabawa jawabin da shugaban kasar Sin ya gabatar yayin bikin bude CIIE karo na 2
2019-11-06 14:18:32        cri

Jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayin bikin bude taron baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na 2 a jiya Talata, ya samu yabo daga al'ummomin duniya, inda suka bayyana shi a matsayin mai karfafa gwiwa.

Shugabannin kasashen da suka hada da Faransa da Jamaica da Serbia da Italiya dama shugabannin kungiyoyin kasa da kasa kamar WTO, da wasu baki a fannin mahalartan bikin sun jinjinawa kudurin kasar Sin na kara fadada bude kofa.

Shugabannin na kasashen duniya sun yi tsokacin ne a jiya, bayan shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawarin kasar za ta inganta bude kofarta ga kasashen ketare a jawabin da ya yi yayin bikin kaddamar da baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na 2 dake gudana a birnin Shanghai.

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya yabawa alkawarin na kasar Sin na fadada bude kofa, yana mai cewa, manufar bude kofa ga kasashen waje da aiwatar gyare-gyare a cikin gida ta kasar Sin, ta samar da sauyi a duniya tare da amfanawa kasar Sin.

Ya kuma alakanta nasarorin da kasar Sin ta cimma da irin kokarinta da kuma tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya, la'akari da cewa kasar ta amfana, kana ta yi tasiri ga tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya bayan shigarta kungiyar raya cinikayya ta duniya, WTO.

Shugaban na Faransa, ya kara da yin kira da daukaka tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban domin magance matsaloli na bai daya da ake fuskanta, da suka hada da rashin daidaito, yana mai cewa, ya kamata kasashe su yi yunkurin hada gwiwa da kuma bude kofa.

Shi kuwa Andrew Holness, Firaministan kasar Jamaica, bayyana bikin baje kolin ya yi a matsayin bayananniyar alama ta kudurin Sin na karfafa hadin gwiwa ta fuskar harkokin cinikayya da zuba jari a duniya.

Ya ce Jamaica ta yi imani da tsarin hadin gwiwar kasa da kasa a matsayin muhimmi, wajen raya tattalin arzikinta. Yana mai cewa, kasar na da buri iri guda da kasar Sin, wato na kara bude kofa da tabbatar da daidadito da dunkulewar tattalin arziki domin moriyar juna da samun ci gaban dukkan kasashen duniya.

Har ila yau, firaministan ya ce ya yi ammana baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na 2, zai kara bude kofa ga karin hadin gwiwa a fannin cinikayya da zuba jari tsakanin kasa da kasa, yana mai kira da a samar da dabara guda ta amfani da fasaha da kirkire-kirkire a harkokin kasuwanci tsakanin kasa da kasa.

A nasa tsokacin, firaministan Serbia Ana Brnabic, wanda ya ce tattalin arziki da harkokin cinikayya na duniya na wani muhimmin gaba a tarihi, ya ce kamar tafarkin da kasar ta ke bi, shi ma kasarsa dake gabashin Turai, ta na kokarin bude kofa da hadin gwiwa maimakon aiwatar da kariyar cinikayya da kulle kofa.

Ya ce kariyar cinikayya da shingayen haraji ko kuma yakin cinikayya, za su kara ta'azzara matsaloli da tabarbarewar al'ummomi, yana mai cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin shi ne misali mafi kyau dake nunawa duniya cewa tattalin arzikin duniya a karni na 21 zai fi samun ingantuwa ta hanyar bude kofa.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Italiya, Luigi Di Maio, ya bayyana baje kolin a matsayin wanda zai samar da dimbin alfanu ga harkokin cinikayya tsakanin kasa da kasa da kuma damarmakin musaya, yana mai jinjinawa kudurin kasar Sin kara bude kofarta ga duniya.

Ya ce kasar Sin muhimmiya ce ta fuskar bada gudunmuwa ga tsarin huldar kasa da kasa.

Shi ma Darakta Janar na hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO Roberto Azevedo, ba a bars hi a baya ba, ya ce baje kolin ya nuna niyyar kasar Sin ta ci gaba da inganta tsarin shigar da kayayyaki daga kasashen ketare da samar da damammakin kasuwanci tare da masu sayayya a kasar da ma duniya baki daya.

Ya ce tattalin arzikin kasashen duniya na dogaro da juna, kuma hanya mafi dacewa ta samun ci gaba shi ne hadin gwiwa. Ya ce bisa yin hakan, za a samar da sahihiyar hanya mai karko da tsarin cinikayya mai sauki da kara dunkulewar tattalin arzikin duniya.

A nata bangaren, mai taimakawa shugaban sashen kula da harkokin kasa da kasa da na jama'a na cibiyar raya masana'antu da kasuwanci ta Najeriya Akintunde Temitope, wadda ke halartar bikin baje kolin, ta ce jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya yi kyau sosai, domin akwai bukatar sauraron irin wannan ra'ayin a yanzu, la'akari da yadda ya bayyana wata makoma mai haske na more nasarori da dama a sabon zamani.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, tsohon ministan harkokin wajen Zambia, Vernon Johnson Mwaanga, ya jinjinawa jawabin shugaba Xi, yana mai cewa, ya kamata a taimakawa kasashe masu tasowa yadda za su rungumi sabuwar fasaha ta hanyar horo da sauran hanyoyin musayar ilimi, domin kada a bar su a baya.

Bayan sauraron jawabin shugaban, Dow Wilson, shugaban kamfanin Varian Medical System, ya ce ya kara samun kwarin gwiwa game da ci gaban kasar Sin, musammam a cikin yanayin rashin tabbas da ake ciki a duniya.

Har ila yau, Pascal Soriot, shugaban kamfanin harhada magunguna na kasa da kasa na AstraZeneca, ya ce jawabin shugaban kasar Sin na kara bude kofa da hadin gwiwa domin samar da al'umma mai kyakkyawar makoma, ya kara nuna kudurin kasar na inganta wani sabon zagayen bude kofa, yana mai cewa sako ne dake karfafa gwiwar kamfanonin kasar da na ketare cewa, Sin ta rungumi tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya da aiwatar da cinikayya cikin 'yanci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China