Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya gabatar da muhimmin jawabi a bikin bude taron CIIE karo na biyu
2019-11-05 17:00:18        cri

A yau Talata 5 ga wata ne, aka bude bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da za a shigowa da su kasar Sin karo na biyu wato CIIE a birnin Shanghai.

A jawabin bude bikin da ya gabatar Shugaban kasar Sin Xi ya jaddada cewa, dunkulewar tattalin arzikin duniya gu daya na tafiya daidai da tarihi. Babu wata kasa da za ta iya warware matsalar bunkasar tattalin arzikin duniya ita kadai, ya kamata kasa da kasa su martaba ra'ayin ba da muhimmanci ga batutuwan da suka shafi rayuwar bil adama, a maimakon fifita muradun kai a kan muradun bil Adama. Kamata ya yi a martaba ruhun bude kofa ga waje tare da daukar matakai masu dacewa, domin sa kaimi ga yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya gu daya. Sa'an nan Xi ya yi kira ga bangarori daban daban da su yi kokari tare wajen raya tattalin arzikin duniya mai salon hadin kai da kirkire-kirkire da ma moriyar juna. Yana mai cewa,

"Kamata ya yi mu hada kai a maimakon zaman 'yan marina, kana mu rushe shingayen da ke raba tsakaninmu a maimakon kafa su, wato mu nuna adawa da ra'ayin kariyar ciniki da na kashin kai. Ban da wannan kuma ya kamata kasa da kasa su inganta hadin kai a fannin kirkire-kirkire, da more sakamakon da aka samu, da ma kawar da shingayen hana mu'ammalar ilmi, fasaha, da ma kwararru. Domin kara kawo alheri ga bil Adama ta hanyar amfani da ilmi, ya kamata mu kare 'yancin mallakar fasaha, a maimakon sanya takunkumi kan ilmi, ko kara gibin kimiyya da fasaha. Ya kamata mu yi kokarin samun makomar ci gaba ta hanyar hakuri da cin moriyar juna, da kiyaye dokoki na kasashen duniya bisa tushen kundin tsarin MDD da makasudin kafa ta da ma ka'idojinta, da martaba babbar ka'idar yin cinikayya tsakanin bangarori daban daban domin sa kaimi ga samar da 'yanci da saukaka harkokin ciniki da zuba jari, ta yadda za a raya yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya gu daya yadda ya kamata, da ma amfana wa dimbin kasashe da al'ummunsu."

Bugu da kari, shugaba Xi ya nanata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba manufar kasar ta bude kofa ga waje, domin yin gyare-gyare da samun bunkasuwa da ma yin kirkire-kirkire a gida, ta yadda za a rika sa kaimi ga aikin bude kofa ga ketare zuwa babban mataki. Xi ya kara da cewa,

"Sin na da babbar kasuwa, muna maraba da kowa da kowa. Sin za ta kara karfin sayen kayayyaki a gida domin raya kasuwarta yadda ya kamata, ta yadda za a mara baya ga ci gaban tattalin arzikin Sin da ma bunkasar tattalin arzikin duniya. Sin za ta mai da hankali kan shigo da kayayyakin cikin kasar, da kara rage yawa harajin da ake karba da ma kudaden da ake kashewa, da kafa wasu yankunan gwaji a wannan fannin, domin kara shigo da kayayyaki da ayyukan ba da hidima masu nagarta daga ketare."

Kawo yanzu dai, Sin ta riga ta sanya hannu kan yarjeniyoyin hadin kai guda 197 tare da kasashe 137 da ma kungiyoyin duniya 30 bisa shawarar "ziri daya da hanya daya". Shugaba Xi ya bayyana cewa, a karkashin ruhun bude kofa ga juna, da samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da kiyaye da'a, Sin za ta martaba ka'idojin yin shawarari tare, da raya aiki tare, da ma more sakamako tare, a kokarin cimma burin amfanawa jama'a da samun dauwamammen ci gaba da ma raya shawarar "ziri daya da hanya daya" yadda ya kamata. Xi yana mai cewa,

"A nan gaba, Sin za ta martaba sabon hasashen samun bunkasuwa, da ci gaba da aiwatar da tsarin yin amfani da kirkire-kirkire wajen ci gaba, da ma inganta aikin canja salon bunkasawa da daidaita tsarin tattalin arziki da kara karfinta domin a raya tattalin arziki yadda ya kamata, gami da samar da dimbin sabbin zarafi ga karuwar tattalin arzikin duniya. Ina da imanin cewa, dole ne Sin tana da makoma mai haske wajen bunkasar tattalin arzikinta."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China