Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#CIIE#Xi Jinping: An tabbatar da kusan dukkan manufofin bude kofa da aka gabatar a bikin CIIE na farko
2019-11-05 10:27:01        cri

An bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu yau Talata a birnin Shanghai, inda Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai taken "Bude kofa da hadin kai don kafa makoma ta bai daya".

A bikin da ya gabata bara, shugaba Xi Jinping ya sanar da matakai 5 na kara bude kofa ga ketare, kuma ya ba da shawarwari 3 ga birnin Shanghai wajen gudanar da wannnan aiki.

Daga cikinsu, an riga an kafa yankin gwaji na yin ciniki maras shinge a sabon yankin Lingang a birnin Shanghai, da kuma kafa kasuwar cinikin takardun hannun jarin kamfanonin kirkiro sabbin fasahohin zamani, wato SSE STAR MARKET a birnin, da aiwatar da tsarin raya yankin Delta na bai daya a matsayin tsarin kasa, ban da wannan kuma, za a aiwatar da dokar zuba jari ta kamfanonin ketare daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar badi, har ma da fitar da wasu manufofin samar da gatanci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China