Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#CIIE#An bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu
2019-11-05 10:07:46        cri

An bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu yau Talata a birnin Shanghai, inda Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarta tare da gabatar da jawabi.

Bikin a wanan karo mai taken "More makomar duniya tare cikin sabon karni" ya samu halartar kamfanoni sama da 3000 daga kasashe ko yankuna fiye da 150, wadanda suka fito daga nahiyoyi biyar, kuma adadin sabbin kasashen ketare da suke shiga bikin ya kai rubu'i. Daga cikinsu kuma, kasashe 10 da suke sahun gaba a bikin ta fuskar girman filin shaguna su ne Amurka, Japan, Jamus, yankin Hong Kong na kasar Sin, Koriya ta kudu, Italiya, Faransa, Austriliya, Switzerland da Birtaniya. Sannan masu sayen kayayyaki sun fito ne daga bangarorin sana'o'i daban-daban, inda 7000 daga cikinsu suka fito daga ketare.

Shugabannin kasa da kasa ciki hadda shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da kuma babban jami'in kungiyar cinikayya ta duniya WTO sun halarci bikin budewar tare da gabatar da jawabi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China