Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin inganta shugabanci a birane
2019-11-04 11:14:34        cri


Shugaban kasar Xi Jinping, kuma sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS, ya jaddada muhimmancin inganta karfin shugabanci da zamanantar da birane.

Xi Jinping wanda kuma shi ne shugaban rundunar sojin kasar, ya bayyana hakan ne yayin rangadin da ya yi a birnin Shanghai, cibiyar hada-hadar tattalin arziki ta kasar , daga ranar Asabar zuwa Lahadi.

Yayin ziyarar rangadin, shugaba Xi Jinping, ya kuma jaddada bukatar nazari da aiwatar da tunanin taro na 4 na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19 da girmama manufar neman ci gaba yayin da ake tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da aiwatar da sabbin dabarun samun ci gaba da gaggauta bude kofa da gyare-gyare da raya tattalin arziki irin na zamani.

Ya kuma bayyana muhimmancin kara matse kaimi wajen inganta ayyukan birane da yin gogayya da inganta karfin shugabanci a biranen na zamani.

Har ila yau yayin ziyarar, shugaba Xi ya gano yadda ake kokarin aiwatar da dabarun zama na 4 na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19, da yadda ake tsarawa da raya birane da gudanar da harkokin shugabanci da bada hidimomi.

Da ya ziyarci wajen samar da ruwa na Yangshupu dake yankin Binjiang na gundumar Yangpu, shugaba Xi ya tabo batun tabbatar da daidaito tsakanin kariya da neman ci gaba, da kuma muhimmancin kiyaye kayayyakin tarihi na birnin.

Ya ce ya kamata a girmama kayayyakin tarihi kamar yadda ake girmama mutanen da suka manyanta, domin samun dorewar tarihi da al'adu birni, ta yadda tarihin zai samu wajen zama a zukatan jama'a, da taimaka musu kara samun kwarin gwiwa kan al'adu da kara kaunar kasa.

Ya ce mutane ne ke gina birane, kuma domin mutane, yana mai cewa dole ne a sanya bukatun jama'a a kan gaba wajen tsarawa da raya birane.

A wata cibiyar birni, a unguwar dake da mazauna daga sama da kasashe da yankuna 50, an yi wa shugaban bayani kan wani dandali na unguwar, wanda ke jin ra'ayoyin mazauna da tattaunawa da wakilansu, dake halartar taron tuntuba kan wani kudurin doka.

Da yake tsokaci game da ayyukan unguwar a matsayin matakin farko na tuntuba na kwamitin gudanarwa na majalisar wakilan jama'a, shugaba Xi ya yi kira da a yi kokarin saukakawa mazauna yadda za su bayyana ra'ayoyinsu bisa samar da wasu hanyoyi, da kuma ci gaba da lalubo nau'ika daban daban na demokradiyya.

Ya ce shugabancin birane muhimmin bangare ne na gaggauta zamanantar da tsari da karfin shugabanci na kasar Sin.

Har ila yau, shugaban ya nanata bukatar mayar da hankali da kai dabarun shugancin birane zuwa gundumomi da al'ummomi, ta yadda za a mayar da hankali kan manyan ayyuka, wadanda suka hada da gina jam'iyya a matakin farko da kula da birane da shugabanci da hidimomin al'umma.

Shugaba Xi Jinping, ya kuma saurari rahoto game da aikin kwamitin JKS na birnin Shanghai da na gwamnatin birnin.

Da yake bayyana bukatar inganta shugabancin birane na zamani, Xi Jinping ya yi kira da a dauki cikakkiyar dabarar tsara birane da ginawa da kula da su da yanayin rayuwa da muhalli da kuma aiwatar da kokarin gwamnati da na al'umma.

Ya bayyana cewa, ya kamata yankin Lingang na cinikayya na gwaji ya aiwatar da manufar zurfafawa da fadada bude kofa ta kowace fuska da karawa wannan aikin karfi.

Ya ce dole ne majalisar kula da kimiyya da fasaha da tsarin bada rajista na yankin gwajin, su jajirce wajen sauke nauyin dake wuyansu, kana ya kamata a kara ingancin kamfanonin da aka zayyana.

Ya ce akwai bukatar Shanghai ta karfafa rawar da take takawa a matsayin cibiyar hada-hadar tattalin arziki da hanyar bude kofa, ta kuma jajirce wajen inganta gyare-gyare da ci gaba da kirkire-kirkire ta hanyar bude kofa.

Game da kara gina jam'iyya, shugaba Xi Jinping ya bukaci dukkan kwamitocin jam'iyyar a matakai daban-daban, su dora a kan sakamakon da aka samu a kashi na farko na gangamin wayar da kai game da burikan shugabannin da suka kafa jam'iyyar da kuma gudanar da kashi na 2 na gangamin cikin kuzari.

Ya ce za a gane nasarar gangamin ne idan ya magance matsaloli, yana mai cewa kashin na 2 zai mayar da hankali ne ga matakan yankuna da warware matsaloli.

Ya ce ya kamata kwamitocin jam'iyyar na matakin yankuna su taka muhimmiyar rawa wajen yayata matsayar jam'iyyar da aiwatar da shawarwarin da ta yanke da jagorantar shugabancin yankunan da hada kan al'umma da kuma inganta gyare gyare da ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China