Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya je ziyarar aiki a birnin Shanghai
2019-11-03 16:15:45        cri

Babban sakataren kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, shugaban kasar, kana shugaban kwamitin soja na kwamitin tsakiyar kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a birnin Shanghai na kasar Sin a jiya Asabar, domin kara saninsa game da yadda ake tsara shirin raya birnin, da gudanar da harkokin unguwanni da kuma ba da hidima ga mazauna birnin, inda ya kuma yi hira da mazauna wurin.

Xi Jinping ya ce, al'ummomin birnin sun gina wannan birni, an kafa wannan birni don tallafawa al'umma. A lokacin da ake gina wani birni, ya kamata mu mai da hankali kan harkokin tallafawa al'ummomi, mu tsara yankin masana'antu, yankin zama da kuma yankin nishadi yadda ya kamata, ta yadda al'ummomin birnin za su ji dadin zaman rayuwarsu.

Ya kuma jaddada cewa, muna gudanar da ayyukanmu cikin yanayin dimokuradiyya a dukkan fannoni, kana, mun zartas da dukkan muhimman kudurori bisa dokokin kasar, sa'an nan, muka fitar da kudurorin bisa nazarin da al'ummomin kasar suka yi cikin hadin gwiwa, da kuma bisa kimiyya da fasaha. Ya kuma kara da cewa, muna fatan al'ummomin birnin Shanghai za su ci gaba da dukufa don ba da gudummawa wajen raya harkokin dimokuradiyya bisa tsarin gurguzu na musamman na kasar Sin. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China