Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da babban jami'in kasar Habasha
2019-10-31 09:31:27        cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana da tsohon shugaban kasar Habasha Mulatu Teshome a ranar Laraba.

A lokacin ganawar da Teshome, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin a matsayin manzon musamman na firaministan Habasha Abiy Ahmed, Wang ya ce kamata yayi bangarorin biyu su zurfafa dangantakar siyasa da amincewa da juna, kuma su baiwa junansu cikakken goyon baya game batutuwan dake shafar muhimman moriyarsu.

Domin fadada hakikanin hadin gwiwarsu, kasar Sin zata karfafawa kamfanoninta gwiwa dasu kara zuba jari a Habasha kuma su kara zurfafa hadin gwiwar gina muhimman kayayyakin more rayuwa, sannan su kara hadin gwiwa da juna game da batutuwan dake shafar shiyya da ma duniya baki daya da nufin kare muradun kasashe masu tasowa, in ji mista Wang.

Ana sa ran babban bakon na Habasha zai yi musayar ra'ayoyi da gwamnatin kasar Sin, da nufin kara zurfafa hadin gwiwa da huldar dake tsakanin bangarorin biyu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China