Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe 54 na goyon bayan matakan Sin a jihar Xinjiang
2019-10-30 19:39:30        cri

Yau Laraba gidan rediyon kasar Sin ya gabata da wani sharhi mai taken "Kasashen duniya kusan 54 suna goyon bayan matakan da kasar Sin ta dauka a jihar Xinjiang", inda aka yi nuni da cewa, kwanan baya a madadin kasashe 54, wakilin kasar Belarus ya gabatar da wani jawabi a yayin taron MDD, inda ya jinjinawa sakamakon da kasar Sin ta samu yayin da take kokarin yaki da ta'addanci da kawar da tsattauran ra'ayi a jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar, lamarin da ya nuna cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu a wannan fannin ya samu amincewar al'ummar kasashen duniya matuka, idan aka kwatanta bayanan wadannan kasashen 54 wato hakikanin yanayin da jihar Xinjiang ke ciki da hadaddiyar sanarwar da kasashen yamma suka fitar wato ra'ayin da bai dace ba, za a fahimci cewa, kasashen duniya wadanda ke goyon bayan kasar Sin sun fi yawa, kuma ra'ayinsu ya fi nuna mutunta hakikanin yanayin ci gaban da jihar Xinjiang ke ciki.

Kana sharhin ya jaddada cewa, dalilin da ya sa wadannan kasashen dunya 54 suka nuna goyon baya ga matakan da kasar Sin ta dauka a jihar Xinjiang shi ne domin sun fi fahimtar sakamakon da kasar Sin ta samu a bangarorin yaki da ta'addanci, da ci gaban tattalin arziki, da bunkasuwar zaman takewar al'umma a jihar, haka kuma suna kyamar ma'auni iri biyu da wasu kasashen yamma suke amfani da su kan batun kiyaye hakkin dan Adam, sun kuma gano cewa, wasu kasashen yamma suna tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe ne ta hanyar fakewa da batun kare hakkin dan Adam, a don haka suna ganin cewa, bai kamata ba a hada batun Xinjiang da manufar siyasa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China