Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa
2019-10-28 19:00:51        cri

Yau gidan rediyon kasar Sin ya gabatar da wani sharhi mai taken "Kasar Sin za ta ci gaba da ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa", inda aka bayyana cewa, kwanan baya shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika wani sakon murnar shirya taron kasa da kasa mai taken "Kara fahimtar kasar Sin" a birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar, inda ya yi nuni da cewa, yanzu duk da cewa an gamu da matsala yayin da ake kokarin habaka cudanyar tattalin arzikin duniya, amma hakan ba zai hana wannan yunkuri ba, saboda kasashen duniya suna da moriya da makoma iri daya, a don haka ya dace al'ummun kasashen duniya su kara kokari domin cimma wannan buri na kara habaka cudanyar tattalin arzikin duniya, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana goyon bayan yunkurin, kuma za ta kara bude kofarta ga kasashen ketare, ta yadda za a ciyar da tattalin arzikin duniya gaba cikin lumana.

Sharhin ya jaddada cewa, bisa matsayinta na kasa mafi saurin ci gaban tattalin arziki ta biyu a duniya, kasar Sin ta samu moriya daga yunkurin habaka cudanyar tattalin arzikin duniya, a sa'i daya kuma, tana ba da gudummowarta, shi ya sa kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye tsarin gudanar da harkokin cinikayya maras shinge, kuma za ta ci gaba da samar da sauki ga masu zuba jari, kana za ta kara bude kofa ga kasashen ketare, a takaice dai ana iya cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba, tare kuma da amfanawa al'ummun kasashen fadin duniya baki daya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China