Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakan kasar Sin na yaki da talauci
2019-11-03 16:20:04        cri

A ranar 17 ga watan Oktoban shekarar 2019 ne, kasar Sin ta yi bikin ranar yaki da talauci na kasa karo na shida, a wannan rana ne shugaban kasar Sin Xi Jinping kana babban sakataren kwamitin koli na JKS, ya jaddada bukatar kara zage damtse wajen ganin an yi nasara a yakin da kasar ta ke yi na ganin bayan wannan matsala.

Shugaba Xi ya ce, wajibi ne kasar Sin ta yi kokarin cimma burinta na kawar da talauci, ta hanyar kara himmatuwa wajen da tabbatar da samun sakamako mai inganci a yaki da talauci.

Haka kuma shugaban ya yaba da irin ci gaban da aka samu, wajen kawar da talauci karkashin jagorancin JKS, yana mai cewa, yakin da kasar take yi da wannan matsala, ya shiga wani muhimmin mataki na ganin an kammala shi tare da samun nasara.

Haka kuma, wajibi ne dukkan yankuna da sassan kasar, su mayar da hankali wajen cimma manufofin da aka sanya a gaba, da ci gaba da kara zage damtse wajen ganin bayan matsalar kangin talauci, da inganta yankunan dake sahun baya a fannin tsarin ba da ilimi tilas, muhimman kayayyakin kiwon lafiya, gidaje da ruwan sha mai tsafta ga al'ummomi masu fama da talauci, da tabbatar da cewa, dukkan masu fama da talauci dake yankunan karkara, sun fita daga talauci, ta yadda nan da shekara mai zuwa, za su shiga rukunin al'umma mai matsakaicin makoma.

A halin yanzu, kasar Sin ta kasance kasar da ta fi fitar da yawan al'umma daga kangin talauci a fadin duniya, kuma ita ce kasa ta farko da ta cimma muradun kawar da talauci da samun bunkasuwa na MDD cikin dukkanin kasashe masu tasowa a duniya. Ta kuma bada gudummawar 70% a aikin kawar da talauci na kasa da kasa. Kana, ya zuwa shekarar 2020, Sin tana fatan kawar da talauci a fadin kasar baki daya.

Masana na cewa, matakin kasar na kawar talauci ya taka muhimmiyar rawa a yakin da ake yi da wannan matsala a duniya baki daya. (Ahmed, Ibrahim /Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China