Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin masana'antun Sin ya gudana cikin lumana a farkon watanni tara na bana
2019-10-23 10:45:35        cri

Jiya Talata 22 ga wata, shugaban hukumar sa ido da yin sulhu ta ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin kuma kakakin watsa labarai na ma'aikatar Huang Libin ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, a cikin farkon watanni tara na bana, tattalin arzikin masana'antun kasar Sin ya gudana cikin lumana.

Jiya yayin taron ganawa da manema labarai da aka kira a nan birnin Beijing, shugaban hukumar sa ido da yin sulhu ta ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin kuma kakakin watsa labarai na ma'aikatar Huang Libin ya bayyana cewa, a cikin farkon watanni tara na bana, wato daga watan Janairu zuwa watan Satumba, tattalin arzikin masana'antun kasar Sin ya gudana cikin lumana, kuma adadin karuwar masana'antun manyan kamfanonin kasar a cikin wadannan watanni tara ya karu bisa kaso 5.6 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, adadin da ya dace da hasashen da aka yi wato kaso 5.5 cikin dari zuwa kaso 6 cikin dari, a cewarsa: "A cikin farkon watanni tara na shekarar da muke ciki, adadin karuwar masana'antun manyan kamfanonin kasar a cikin wadannan watanni tara ya karu bisa kaso 5.6 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, adadin da ya dace da hasashen da aka yi wato kaso 5.5 cikin dari zuwa kaso 6 cikin dari, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin ta samu kyautatuwa a bangaren gyara tsarin masana'antun kasar da kuma ingiza ci gaban masana'antun. Duk da cewa, ana fuskantar matsaloli daban daban a gida a kasar Sin da kuma kasashen ketare tun daga farkon bana, hukumomin da abin ya shafa a fadin kasar suna kokari matuka karkashin jagorancin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar, domin dakile hadari da kalubalen da suke fuskanta, haka kuma sun cimma burin tabbatar da gudanar tattalin arzikin masana'antu lami lafiya, a takaice dai ana iya cewa, ci gaban tattalin arzikin masana'antun kasar Sin ya dace da hasashen da aka yi, har ya samu sakamako mai gamsarwa."

Hakikanin alkaluman da aka samu sun nuna cewa, a cikin farkon watanni tara na bana, muhimman sana'o'in kasar sun fi samun ci gaba, misali adadin karuwar masana'antun kamfanonin samar da danyen kayayyaki ya karu da kaso 7 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, kana muhallin kasuwancin kamfanoni yana ci gaba da samun kyautatuwa sannu a hankali, ban da haka adadin karuwar tattalin arzikin kamfanoni masu zaman kansu na kasar ya karu da kaso 8 cikin dari, haka kuma adadin karuwar tattalin arzikin kamfanoni matsakaita da kanana ya kai kaso 7.1 cikin dari, hakazalika karfin ci gaban tattalin arzikin zaman takewar al'ummar dake karkashin goyon bayan sana'o'in sadarwa da manhajarsu, shi ma yana kara karfafuwa, musamman ma a bangaren amfani da fasahar 5G, ya zuwa karshen watan Satumban bana, manyan kamfanonin sadarwar kasar Sin wato China Mobile da China Unicom da kuma China Telecom sun riga sun gina tasoshin 5G sama da dubu 80 a fadin kasar Sin, a sa'i daya kuma, ana amfani da fasahar a fannonin samar da murya da bidiyo masu inganci na AR da VR da kuma samar da na'urorin da ake amfani da su a cikin mota, nan gaba kuma za a kara yin amfani da su a fannonin masana'antu da aikin likitanci da kuma samar da makamashi.

Jami'in ya kara da cewa, yanzu haka ana fama da matsala yayin da ake kokarin raya tattalin arzikin duniya, kuma sana'ar kere-keren kasar Sin ita ma tana fuskantar kalubale saboda tana yin gyara fuska domin samun kyatatuwa, yana mai cewa, "A farkon bana, mun yi hasashe cewa, ya dace adadin karuwar attalin arzikin masana'antun manyan kamfanonin kasar Sin ya karu bisa kaso 5.6 zuwa 6 cikin dari, duk da cewa adadin karuwar a bara ya kai kaso 6.2 cikin dari, amma mun tsara shirin ne bisa hakikanin yanayin da muke ciki, kuma mun lura cewa, domin cimma burin, bangarorin da abin ya shafa sun yi kokari matuka."

Jami'in ya jaddada cewa, nan gaba ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatin kasar domin ingantawa da karfafawa da kuma ciyar da masana'antun kasar gaba yadda ya kamata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China