Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da taron mika 'yancin mallakar ilimi na kasa da kasa a Beijing
2019-10-21 10:44:52        cri

 

A jiya Lahadi, aka kaddamar da taron mika 'yancin mallakar ilimi na kasa da kasa a birnin Beijing na kasar Sin, taron da za a kwashe kwanaki 3 ana gudanar da shi.

Wannan gagarumin taro ya samu halartar wakilan hukumomi fiye da 300 na gida da na ketare, wanda ke da manufar raya harkar mika 'yancin mallakar ilimi a kasar Sin, don kara yin amfani da 'yancin yadda ake bukata ta yadda zai taimakawa kokarin raya tattalin arziki, gami da kafa wani dandali mai kyau a fannin mika 'yancin mallakar ilimi.

Hakika 'yancin da ake da shi wajen mallakar ilimi shi ne ginshikin raya tsarin kasuwanci a wata zamantakewar al'umma ta gurguzu, kana ba za a rasa shi ba, idan ana son kirkiro sabbin fasahohi, da raya cinikin kasa da kasa na samar da hidimomi, da yada al'adun gargajiya masu kyau na al'ummar Sinawa, gami da biyan bukatun jama'ar kasar na neman samun zaman rayuwa mai kyau.

A wajen bikin bude taron, Yu Cike, shugaban hukumar kula da 'yancin mallakar ilimi karkashin sashin kula da harkar yada labarai na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin, ya ce gwamnatin kasar Sin tana dora cikakken muhimmanci kan kare 'yancin mallakar ilimi, saboda haka aka sanya taken taron wannan karo ya zama " Kokarin kare madaidaicin ra'ayi gami da kirkiro sabbin fasahohi, tare da neman hadin gwiwa don tabbatar da moriyar dukkan bangarori".

"Yadda ake gudanar da taron don mika 'yancin mallakar ilimi zai sa a yi amfani da bayanan da ilimi da ake da su a kasarmu yadda ya kamata, ta wannan hanya ana dogaro kan kasuwanni wajen raba albarkatun raya tattalin arziki. Za mu kara goyon bayan wadanda ke da niyyar zuba jari don yin amfani da ilimi da bayanai, da taimakawa shirya tarukan mika 'yancin mallakar ilimi a wurare daban daban, ta yadda a karshe za a kafa wani cikakken tsarin mika 'yancin a kasar Sin, don raya harkar kare 'yancin mallakar ilimi yadda ake bukata."

Wannan taro ya riga ya zama wani dandali mai kyau na nuna wa mutanen duniya ilimi da bayanai mallakar kasar Sin, inda ake baiwa baki mahalarta taron damammakin musayar ra'ayi gami da nuna bayanai da abubuwa na fannonin kayayyakin tarihi, da fina-finai, da majigin yara da wasanni, da bayanan shafukan yanar gizo ta Internet, da dai makamantansu. Sauran ayyukan da za a gudanar wajen taron sun hada da taron tattaunawa, da nune-nunen fasahohi, da bukukuwan sanya hannu kan yarjejeniya, da na ba da kyaututuka, da dai sauransu. A nashi bangaren, karamin jakadan kasar Koriya ta Kudu a kasar Sin, Han Jae-Kwon, ya ce,

"Kasar Koriya ta Kudu ita ma ta yi kokarin halartar taron na wannan karo, akwai kamfanonin kasarmu guda 18 da suke nuna fasahohinsu. Haka kuma za mu gudanar da wasu taruka a gefen wannan taron, da nufin habaka hadin kai tsakanin kamfanonin Sin da na Koriya ta Kudu."

A wajen taron na wannan karo, ana mai da hankali sosai kan mai da ilimi da bayanai su zama masu amfanawa ci gaban tattalin arziki, don haka aka baiwa kamfanonin sana'o'i daban daban cikakkiyar damar musayar ra'ayi don neman kulla huldar hadin kai. Feng Wei, babban darektan yankin Sin na hadaddiyar kungiyar tsara fina-finai ta kasar Amurka, ya tabo maganar hadin gwiwa kan harkar fina-finai.

" Ana samun ci gaba cikin sauri a kasuwannin fina-finan kasar Sin, saboda haka yanzu ana mai da hankali sosai kan raya cinikin kayayyaki masu alaka da fina-finai a kasar."

A jiya Lahadi, mahalarta taron sun gane ma idanunsu yadda aka kafa wasu hukumomi a karkashin kawancen cibiyar cinikin 'yancin mallakar ilimi ta kasar Sin, da kaddamar da wani kawance na kare 'yancin mallakar ilimi gami da cinikin ilimi tsakanin kasa da kasa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China