Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bincike:Kasashe masu tasowa na daukar kasar Sin a matsayin mai ba da gudummawa ga ci gaban duniya
2019-10-18 19:25:44        cri
Wani sabon rahoton bincike da aka wallafa a yau Jumma'a na nuna cewa, kimanin kaso 60 cikin 100 na wadanda aka zanta da su daga kasashe masu tasowa, suna daukar kasar Sin a matsayin mai ba da gagarumin gudummawa ga ci gaban duniya.

A cewar rahoton, mutane 11,000 daga kasashe 22 ciki har da kasar Sin, mutane 500 da aka zanta da su a wadannan kasashe, sun halarci wani bincike da cibiyar nazarin harkokin kasar Sin da na duniya da Kantar ta gudanar, wani kamfanin tuntuba da adana bayanai na kasa da kasa, daga watan Mayu zuwa Yulin shekarar 2018. Wadanda aka zanta da su, suna tsakanin shekaru 18 da 65.

Rahoton ya bayyana cewa, galibin sassa 7 da aka yi amfani da su wajen bayyana kasar Sin da bincike ya zayyana, suna nuna kasar dake gabashin Asiya a matsayin kasa mai dogon tarihi da abubuwan mamaki, inda kaso 59 cikin 100 na wadanda aka ji ra'ayoyinsu daga kasashen ketare suka amince da wannan sakamako. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China